“Na fi yin rubutu akan abubuwan da marubutanmu ba su fiye yin rubutu akai ba”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
(Ci gaba daga makon jiya)
Marubuciya Na’ima Sulaiman Daƙayyawa ba ɓoyayyiya ba ce a tsakanin matasan marubutan Hausa a Jihar Jigawa. Ta fito ne daga ƙaramar Hukumar Kaugama. Tana da gogewa a harshen Larabci da Hausa, inda yanzu haka take karatun digirinta na biyu a Jami’ar Sule Lamiɗo dake Kafin Hausa. Marubuciya ce da ta bambanta da sauran marubutan adabi, saboda ita ta fi mayar da hankali ne kan muhimman abubuwa na tarihi ko al’adu. Akasari rubuce-rubucen da ta yi sun shafi zamantankewar al’umma ne da tarihinsu. Littafin ta na farko, ‘Daƙayyawa Tsakiyar Kano’ ya samu karɓuwa sosai a wajen jama’a kuma ya buɗe mata ƙofar samun ɗaukaka da albarka a rayuwarta. A zantawarta da Abba Abubakar Yakubu ta shaida masa babban burinta na rayuwa. A yi karatu lafiya.
MANHAJA: Kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa?
NA’IMA SULAIMAN: Kawo yanzu na rubuta littattafai sun kai guda goma, wasu na kammala har sun fita ga jama’a wasu uma ina kan aik a kansu. Sun haɗa da littafin, ‘Daƙayyawa Tsakiyar Kano’, ‘Rana ɗaya’, ‘Yaye’, ‘Sankarar Mama’, ‘Kuɗin Ritaya’, ‘Karin Harshe A Masarautun Jigawa’, ’Yalleman Garin Waliyan Allah’, ‘ƙwalamammiya’, ‘Bara Akufai’, ‘Barin Halak Don Kunya’, da kuma ‘Farautar Mutunci’. Sai dai kuma akwai gajerun labarai da na yi da dama. Ina ɗauko abubuwan da suka shafi zamantankewa, musaman game da wata matsala da take faruwa, ko take damun al’ummarmu sai dai kuma a wasu lokutan ba a fiya ɗaukarsu a matsayin matsala ba.
Daga ciki akwai labarin da na rubuta mai suna ‘Yaye’, wanda labari ne da ke nuna yadda iyaye mata suke yaye yara ƙanana, kuma suke amfani da maganin barci wajen hana yaro kukan dare, don gudun kar ya tashi yana neman mama. Akwai wasu iyayen da ke bai wa jariransu maganin sa barci wanda zai bugar wa da yaro ya yi ta barci, ba tare da ya fitini uwar da kuka cikin dare ba. Ka ga a nan uwa da kanta ta koya wa ɗanta shan kayan maye tun yana ƙadamin da bai san kansa ba. Hakan illa ce babba, sai dai ba kowacce uwa ce za ta fahimta ba.
Akwai kuma littafin ‘Farautar Mutunci’, wanda labari ne da ya shafi yadda al’umma ke kallon ‘ya mace bazawara. Daga lokacin da wata ƙaddara ta sa mace ta fito daga gidan mijinta to, daga nan ne wasu maza a gefe, ‘ya’yan Allah bani, za su fara kai miki farmaki, ko da kuwa baki da ra’ayin aikata abin da ba daidai ba. Amma ta ƙarfi da yaji sai sun yi ta ƙoƙarin ɓata miki syna da mutuncinki ko ta halin ƙaƙa, wanda ni ɗin nan ganau ce ba jiyau ba, sai dai in Allah ne Ya taimake ki ki ka sha da ƙyar.
Sannan shi littafin ‘Sankarar Mama’ yana magana ne kan yadda ciwon ya ke yin illa mai girman gaske a jikin ýa mace da yadda mutanan mu na karkara ba su farga da illolin ciwon ba, har ta kai ga dubban mata suna rasa ransu a dalilin sankarar mama.
Kin taɓa wallafa wani daga cikin littattafan da ki ka rubuta?
E, na buga littafina na farko, wanda nake yi wa kirari da ɗan albarka, wato littafin ‘Daƙayyawa Tsakiyar Kano’, wanda shi ne ya sa aka fara sani na, kuma ya kawo min alheri mai yawa.
Mene ne ya ja hankalinki ki ka rubuta wannan littafi na Daƙayyawa Tsakiyar Kano?
Kishin garin mu Daƙayyawa ne ya jawo haka, kuma shi ne sila. Zan iya tunawa akwai wani malaminmu da ya bamu aikin gida a lokacin ina karatun digirina na farko, akan kowa ya rubuta masa tarihin anguwarsu. To, da na je ina rubuta Tarihin Unguwar Turaki sai na ga cewa to, wai unguwa ɗaya tana da wannan tarihin ina ga shi kuma garin Daƙayyawa ɗin kansa! Wanne irin tarihi ne da shi? Wannan shi ne mafarin abin da ya zaburar da ni na ga ya kamata in faɗaɗa bincikena kan tarihin garin Daƙayyawa bakiɗaya. Daga nan ne na ɗaura ɗamarar nemo tarihin daga bakunan magabata, ta kowanne lungu da saƙo.
A lokacin da sauran marubuta adabi musamman mata ke rige-rigen rubutu kan soyayya da zamantakewar aure, ke me ya sa ki rubutu kan tarihi, fannin da ba a cika damuwa da shi ba?
Wannan shi ne matakin nasarar tawa. A wasu lokuta ina kallon abin da mutane basu fiye la’akari da shi ba, wanda kuma idan an bankaɗo shi abu ne da sai an sha mamaki. Yanzu akwai littafin da na ke kan rubutawa mai suna ‘Kuɗin Ritaya’ wanda na san in dai ya kammala mutane da yawa za su yi alfahari da rubutun, musaman iyaye da kakanni, kai da duk wani ma’aikacin gwamnati ma.
Lokacin da ki ka ƙaddamar da littafinki wanne goyon baya ki ka samu, kuma ya za ki kwatanta alherin da ki ka samu a lokacin?
Kamar yadda muka sani, ‘ya mace a kodayaushe mai rauni ce, wasu nasarorin kuwa basa zuwa mata dole sai da goyan bayanwani namiji tsayayye, kamar iyayenta, ko wani shaƙiƙin ɗan’uwanta ko kuma ma dai mijinta. Sai dai ni a nawa ɓangaren na samu goyan baya ne daga iyayena a matakin farko.
Amma kuma akwai wasu mutanan da suka zame min tsani wajen ganin na kai ga matakin nasara, irin su Farfesa Mu’azu Sa’adu Kudan, Dakta Ginsau Abdulƙadir Haɗejia, da kuma ubangayya wanda a wajensa ne na samu cikken goyan baya, kuma ba don shi ba wataƙila da ba a ƙaddamar da littafin ba, shi ne Alhaji Haladu Aliyu Madaki Daƙayyawa. Sai kuma jajirtattun ‘yan kwamitina da suka taimaka min wajen ƙaddamar da littafin, waɗanda mutane masu dama da yawansu ya kai kimanin mutum 40, don haka ba zai yiwu na ambaci sunayensu ba. Lallai babu shakka na ga soyayya a wajen al’ummar garinmu.
Kawo yanzu wanne littafin ki ke rubutawa, kuma a wanne matakin ki ke? Na onlayin ne ko shi ma bugawa za ki yi?
Kamar yadda na faɗa a baya ina aikin rubuta wani littafi mai suna, ‘Kuɗin Ritaya’, akwai kuma littafin ‘Karin Harshen Mutanen Masarautun Jigawa’, da kuma littafin, ’Yalleman Garin Waliyan Allah’. Idan ka lura littattafai ne na tarihi da kuma nazari kan binciken da nake gudanarwa.
Sannan akwai gajerun labarai da nake kan cigaba da rubutunsu akai-akai. Don ba na iya sati guda ban rubuta wani labari ba.
Ko za ki gaya mana yadda shafukan sada zumunta ke taimaka miki wajen yaɗa rubuce-rubucenki, da ganawa da masu bibiyar labaranki.
Shafukan sada zumunta su ne matakin farko wanda nake aika saƙona ga al’umma, kuma su isa nan take ba takere da samu wani tsaiko ko jinkiriba. A dalilin haka ne ma na ƙirƙiri gidan Talabijin wanda muka fara ɗora shirye-shiryenmu a kai. Muna ma kuma da shafi a manhajar TikTok da Facebook da kuma a Whatsapp Channel.
Kina ganin mene ne ya bambanta ki da sauran marubuta da ke ƙoƙari a fagen adabin Hausa?
Na fi yin rubutu akan abubuwan da marubutan mu ba su fiye yin rubutu a kai ba, don ni rubuce-rubuce na sun fi alaƙa da harkar Ilimi musaman saboda yara masu tasowa su amfana.
Ban da rubutu, wacce baiwa ki ke da ita wacce da dama mutane ba su san ki da ita ba?
Babban alherin da na samu shi ne yadda Sarkin Hadejia Mai Martaba Alhaji Adamu Haruna Maje CON ya shafe tsawon minti 30 yana min addu’a. Wannan ba ƙaramin alheri ba ne, sunana ya watsu ya je inda ban taɓa tunanin zai je ba, shi ma wannan alheri ne. Haɗuwa da waɗanda nake ganin ban taɓa zaton zan haɗu da su ba, ban da yadda lalitata ta cika da matsabbai, wanda har gobe hakan na faruwa, sai kuma alfarma da shiga inda ban taɓa zaton ƙafata za ta shiga ba a dalilin littafin nan na shiga. Shi ya sa nake kiran littafin ɗan Albarka Mai Albarka.
Shin kina da ra’ayin shiga siyasa a rayuwarki?
Ba zan ce ba ni da ra’ayi ba, a wasu lokutan abubuwa suna zuwa ne bagatatan, domin shi Ilimi babu inda ba ya kai mutum, amma dai ina sha’awar zama Farfesa a Harshen Larabci, in sha Allahu.
Wanne abu ne ya fi ɗauke miki hankali idan kina zaune ba kya komai?
Abubuwan suna da yawa. ƙalubalen rayuwa, na kan sa wasu lamura a mizani ina aunawa, shin haka za a yi? Haka za mu cigaba da tafiya? Yarana mata ne har uku. Ba ni ke ɗawainiya da su ba mahaifiyata ce. Mahaifina kuma shi ke jan akalar kula da rayuwata da ta su, amma sha’anin ya kan ɗauke min hankali ina shafe tsawon awanni kan tunanin inda ba sa nan to, da yaya zan yi kenan a wannnan duniya? Mahaifana su ne burina na farko.
Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?
Mai haƙuri shi ya kan dafa dutse har ya sha romonsa.
Na gode.
Ni ma na gode da wannan dama da aka ba ni.
