Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi ta jaddada ƙudirin ta na kulawa da iyalan ‘yan sanda da suka rasu a bakin daga yayin artabu da ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar mulki ta Sakaba.
Ya yi wannan bayanin ne jiya a fadar gwamnatin jihar yayin da ya ke karɓar baƙuncin wata tawaga daga ofishin Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya Mista Olatunji Disu ƙarƙashin jagorancin mataimakin Sufeto Janar Umar Dada don jajentawa gwamnati da kuma al’ummar jihar Kebbi.
Gwamna Malam Nasir Idris ya jajentawa rundunar ‘yan sanda tare da bayyana cewa rayuwar su ba ta tafi a banza ba saboda sun rasu ne wajen kare martabar ƙasa da kuma al’umma.
Ya ƙara da cewa al’adar Gwamnatin jihar Kebbi ce ta tallafawa iyalan jami’an da suka rasu a bakin daga saboda haka su ma gwamnati za ta tallafa wa iyalan su a duk lokacin da hakan ta taso.
Tun farko da ya ke jawabi, Mataimakin Sufeto Janar Umar Dada, ya bayyana cewa sun zo ne a madadin Sufeto Janar don jajentawa ga Gwamnati da kuma al’ummar jihar Kebbi bisa ga rasa jajirtattun jami’an yan sanda sanadiyyar kare martabar ƙasa da kuma al’umma da kuma dukiyoyin su.
Ya tabbatar wa gwamnan da cewa rundunar yan sanda ba za ta zauna ba har sai ta zaƙulo duk waɗanda ke da hannu a cikin wannan aikin ta’addanci tare da gurfanar da shi domin fuskantar shari’a.
Ya yaba wa gwamna Nasir Idris bisa ga irin ƙoƙarin da ya ke yi na gudummawa ga rundunar ‘yan sanda a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso tare da ba shi tabbacin ba da daɗe wa ba rundunar ‘yan sanda za ta samar da wata runduna ta musamman don inganta tsaro a jihar.
