JAMB ta zayyano kurakurai da ɗaliban UTME da DE kan yi yayin shigar da bayanansu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Haɗaka ta Shirya Jarrabawar Ɗalibai masu neman shiga Manyan Makarantu (JAMB), ta gargaɗi ɗalibai akan kurakuran da ka iya haifar musu da tsaiko da suke yi yayin shigar da bayanansu domin rubuta jarrabawar Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) ko rajistar Direct Entry (DE).

A cewar JAMB, kuskure guda a matakin ka iya samar da babbar matsala yayin neman gurbin shiga babbar makaranta ta hannunta.

JAMB ta bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ta fitar domin bayar da shawara ga waɗanda hakan ya shafa, wanda ta yi wa laƙabi da “JAMB Ekplained” a kafar X, ranar Laraba.

An fitar da saƙon ne da nufin wayar da kan sababbin ɗalibai, inda ta ce kurakurai wajen rubuta suna da lokacin haihuwa ababe ne da ka iya haifar da tsaiko yayin neman gurbin karatu a manyan makarantu.

Akan haka ne ta shawarce su da su riƙa dubawa tare da tabbatar da komai da suka rubuta ya yi daidai kafin shigarwa, musamman wajen la’akari da bayanan da lambobin katin shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) ke ɗauke da su sune mutum ya sanya.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, dukkan wani bayani da ya ƙunshi suna ko kwanan watan haihuwa ba daga gare ta ba ne kai-tsaye, saidai hakan na ƙunshe ne a kundin hukumar kula da lamuran samar da NIN (NIMC).

Ta ƙara da cewa, koda ɗalibi ya nemi gyara wani bayani daga NIMC, hakan ba zai bayar da damar sauyawa, tana mai gargaɗin ɗalibai da su kiyaye ƙa’idoji da sharuɗɗan hukumar yayin rajista.

By Babaji

Leave a Reply