
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa NiMet, ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama mai ɗauke da tsawa a sassan jihohin Nijeriya da tsawa a ranar Laraba, 12 ga Agusta, 2026, don haka ne ta shawarci mazauna a wuraren da ke fuskantar barazanar ambaliya da su kasance a ankare.
A wani saƙon hasashen yanayi na kullum da NiMet ta wallafa a kafar X a ranar Talata, hukumar ta ce ana tsammanin samun hadari a jihohin arewacin Nijeriya da safe, tare da tsawa da matsakaicin ruwan sama a Adamawa, Taraba, Bauchi, Gombe, Jigawa, Kaduna da kuma Kano.
Da lokacin rana kuwa, hukumar ta yi hasashen samun matsakaicin ruwa a sassan jihohin, Kaduna, Katsina, Kano, Kebbi, Zamfara, Sakkwato, Yobe, Bauchi, Borno Adamawa da Taraba.
A jihohin tsakiyar Nijeriya kuma, NiMet ta ce akwai yiwuwar da safe a samu tsawa da matsakaicin ruwan sama a sassan Nasarawa, Benuwai, Kogi da Birnin Tarayya Abuja.
Haka kuma, NiMet ta ce ana sa ran samun tsawa da matsakaicin ruwan sama a sassan shiyyar a lokutan rana da kuma dare.
Ga jihohin kudanci, NiMet ta yi hasashen hadari da safe tare da yiwuwar yayyafi a sassan Jihar Ondo da kuma shiyyoyin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.
A lokutan rana da dare, yayyafi ake tsammanin samu a sassan Kuros Riba da Akwa-Ibom, yayin da ake sa ran matsakaicin ruwan sama a sauran sassan shiyyar kudancin Nijeriya.
Don haka ne hukumar ta kirayi mazauna masu ababen hawa, masu gudanar da harkokin jiragen sama da su ɗauki matakan kariya, tana mai gargaɗin samun iska mai ƙarfi tare da tsawa a lokacin.
