Musa Funtua ya ƙaddamar da ƙungiyar Gwagware Continuity a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan Lafiya na Jihar Katsina,Hon Musa Adamu Funtua,ya ƙaddamar da ƙungiyar a garin Funtua sa mai suna Gwagware Continuity dan samun nasarar zaɓen 2027.

Hon Musa Adamu ya bayyana mutanen da suka samar da ƙungiyar a matsayin mutane masu mutunci da kima ga al’ummar Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya, dan haka babu ko shakka akwai gagarimar nasara a wannan tafiya ta samun nasara ga ‘yan takarar jamiyyar APC tunda sama har ƙasa, nji Hon Musa Adamu Funtua.

Kwamishinan mai riƙe da sarautar Ɗan Kafin Katsina,ya kuma tabbatar da cewa,daga yau wannan ƙungiyar babu sauran zama,sai fafutukar yadda zamu samu nasarar zaɓen 2027.

Kuma muna godiya ga Allah ya sanya duk inda zamuje neman alfarma muna da abinda zamu nuna na ayyukan Gwamna Dikko Raɗɗa da ya yi wa al’ummar Jihar Katsina.Wannan haja tamu sayayyace ga al’ummar Jihar Katsina baki ɗaya.

Da ya koma kan batun ayyukan da Gwamna Dikko Raɗɗa ya yiwa al’ummar ƙaramar hukumar Funtua,Hon Musa Adamu ya bayyana cewa,hatta ‘yan jamiyyun adawa sun sallama a kan ayyukan gwamna Dikko Raɗɗa a ƙasa ba labari ba.

Hon Musa Adamu ya kuma tabbatar da cewa,duk wanda ya nemi kawo ma tafiyar ƙungiyar Gwagware Continuity 2027, zagon ƙasa to lallai zai gamu da dakaru da za su tarwatsashi ko wane , mun shirya.inji Hon Musa Adamu Funtua.

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar na Jihar Katsina (MAN) For Gwagware Continuity 2027, Kwamred Mannir Suleman Funtua, ya bayyana ayyukan da ƙungiyar ta gabatar na taimaka al’ummar Jihar Katsina,wanda suka haɗa da ,tallafa wa marasa lafiya,marayu ,ɗaliban firamare ,da suka basu kayan makaranta,samar da guraben karatu a , jami’oi, kwalejin kimiya da fasaha , Kwalejin Kiwon lafiya da sauran manyan makarantu.

Kwamred Suleiman Funtua ya tabbatar da cewa,hatta lokacin watan azimin Ramadan da ya gabata ƙungiyar MAN ta tallafa wa al’ummar da abincin buda baki a faɗin Jihar Katsina. Sai kuma allular rigakafin ƙarzuwa a makarantun tsangaya da ba su magunguna kyauta.Inji Kwamred Mannir Suleman.

Da yake nasa jawabin jigo a ƙungiyar MAN, Alhaji Nura Suleman “Yanɗaki ya bayyana cewa, lokaci yayi na mu fito dan mara wa ,Hon Musa Adamu goyan baya a kan manufofinsa na alheri da cika masa burinsa na ganin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya ci zaɓe karo na biyu, da dukkan ‘yan takarkarun jamiyyar APC tun daga sama har ƙasa.inji Alhaji Nura Suleiman”.

“Nura “Yandaki ya tabbatar da cewa, ƙungiyar ba ta fito ba sai da ta shirya tsaf dan shiga saƙo da lungo wajen wayar da kan al’ummar Jihar Katsina kan zaɓar gwamna Dikko Raɗɗa a zaɓe na 2027 da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu.

A ƙarshen sakatare ƙungiyar MAN, Alhaji Shamsu ya bayyana godiyar ga mambobin ƙungiyar da suka halarci wannnan gagarimin bikin ƙaddamar da ƙungiyar MAN dan samun nasarar gwamna Dikko Raɗɗa a zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply