Shekarau ya buƙaci a samar da ƙarin damarmaki ga matasa bayan ɗaukar nauyin yaye ɗaliban NCE 830

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Aƙalla ɗalibai guda 830 ne tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ya ɗauki nauyin yaye su bayan kammala karatun NCE daga Community College of Education da ke Kano, a wani yanayi na bunƙasa ilimin malamai da inganta ɗan-adam a jihar.

A safiyar ranar Asabar ne aka gabatar wa ɗaliban shaidar kammala karatun nasu, wanda aka gudanar a ɗakin taro na School of Arabic Studies (SAS) a Kano, wanda kuma ya kawo nasarar kammala shirin ɗaukar nauyi karatu da Shekarau ya samar a 2022 a lokacin da yake ɗan Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Kakakin tsohon gwamnan, Farfesa Sule Ya’u Sule ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar, inda ya ce an tsara shirin ɗaukar nauyin karatun ne da nufin faɗaɗa hanyoyin samun ilimin malamai ga matasa a Gundumar Kano ta Tsakiya.

A cewarsa, shirin ya ƙunshi ɗalibai daga ƙananan hukumomi 15 na yankin, inda aka ɗauki mutum 50 daga kowacce ƙaramar hukuma, lamarin da ya kai jimillar adadinsu zuwa 750.

Ya bayyana cewa, Shekarau ya kuma faɗaɗa shirin da ƙarin wasu ɗalibai 100 na Kwalejin Ilimin waɗanda suka gaza biyan kuɗin karatu, wanda hakan ya mayar da jimillar zuwa 850.

Daga cikin waɗanda aka ɗauki nauyin nasu, 830 sun yi nasarar kammala karatu kuma sun karɓi takardun shaidarsu, yayin da 15 kuma suka samu faɗuwa a wasu darussa da sai sun maimaita su, sai kuma wasu biyar da suka fice daga cikin shirin.

Farfesa Sule ya ƙara da cewa, Shekarau ya bayyana gamsuwa da sakamakon da aka samu a sanadiyyar shirin, yana mai jaddada aniyarsa ta cigaba da ɗaukar nauyin shirin domin bai wa matasa damar samun ilimi mai inganci a jihar.

By Babaji

Leave a Reply