NLC ta ayyana shiga yajin aiki bayan zargin Kwamishinan Delta da umarnin lakaɗa wa mataimakin darakta duka har lahira

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An samu wasu bayanai masu alaƙa da mutuwar Mista Unity Ekpevbughe Adeda, Mataimakin Darakta a Ma’aikatar Ilimin Sakandare ta Jihar Delta, wanda aka yi zargin ya rasu bayan lakaɗa masa duka bisa umarnin Kwamishinan, Dakta Kingsley Ashibogwu.

Bayan haka ne Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), reshen Jihar Delta ta ayyana tsunduma a yajin aiki. Shugaban NLC a jihar, Goodluck Oforbruku ne ya sanar da haka a ranar Juma’a yayin jawabi ga ma’aikata masu zanga-zanga a Sakatariyar Chike Edozien da ke Asaba.

Oforbruku ya ce matakin nasu amsa ne ga abin da ya bayyana a matsayin mummunan kisa ba bisa doka ba akan babban jami’in gwamnati da ke bakin aiki. A baya ne dai ma’aikata a sakatariyar jihar suka rufe farfajiyar bisa zanga-zanga bayan fitar labarin mutuwar Adeda.

A cewar shaidu daga ma’aikata, an yi zargin an ɗaure mamacin ne tare da lakaɗa masa duka babu tausayawa daga wasu ɓata-gari da aka ce sun yi haka ne bisa umarnin Kwamishinan, inda kuma aka yi zargin har da hannun ‘yan sanda da direbansa acikin al’amarin. An ce, Adeda ya rasu ne jim-kaɗan bayan faruwar al’amarin.

Wannan al’amari dai ya tayar da ƙura acikin ma’aikatan jihar, inda jagororin ƙwadago suke kira da a gaggauta gudanar da bincike, kame da gurfanar da dukkan waɗanda aka samu da hannu a cikin faruwar al’amarin.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sanda, gwamnatin jihar ko ma’aikatar ilimi ba su fitar da wani saƙo kan al’amarin ba.

By Babaji

Leave a Reply