Talakawan Nijeriya na amfana da gyare-gyaren tattalin Tinubu, inji Ministan Labarai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris Malagi, ya ce baki ɗaya ‘yan Nijeriya suna amfana da gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take yi ba tare da la’akari da bambance-bambancen zamantakewa ko siyasa ba. Ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa mutane ƙalilan ne suke amfana daga gyare-gyaren, inda ya ce hatta talakawa suna amfana.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, 2026 yayin wayar da kan ‘yan jarida gabanin ƙaddamar da manufofin jam’iyyar APC ga zaɓukan 2027, inda ya ƙara da cewa ƙungiyoyin ƙasa-da-ƙasa da hukumomin bayar da maki sun yi wa tattalin Nijeriya kyawawan shaida.

“Sau da yawa mutane suna yawan cewa baki ɗaya waɗannan gyare-gyare suna faruwa, amma mutane kaɗan ne suke amfana daga gare su,’ Kuma sai nake yin wannan tambayar: A lokacin da aka haɗa hanyar Abuja zuwa Kano, ba a ce min sai wani ya nuna katinsa na zama ɗan APC ba ko mai kuɗi ko kuma shi ɗan wani aji ne cikin mutane kafin a bar shi ya wuce ta nan,” inji shi.

Ya kuma tunatar da masu kokwanton nasarorin Shugaba Tinubu a fannin tsaro musamman yadda aka shiga fargabar halin a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, yana mai cewa a yanzu babu ‘yan bindiga da ke addabar mutane a yankin bisa ƙoƙarin da gwamnatin ta yi wajen shawo kan matsalar.

Kazalika, Ministan ya ce kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 1.6 ne suke amfana daga Shirin Bayar da Lamunin Karatu ga Ɗaliban Manyan Makarantu (NELFUND), wanda shaida ne kan cewa talakawa na amfana da gyare-gyaren gwamnatin Tinubu.

A nasa jawabin, Ministan Kasafi da Tsara Tattali, Atiku Bagudu, ya ce ajandar gyare-gyaren Tinubu an kafa ta ne bisa hangen nesa ga Nijeriya da ƙoƙarin warware ƙalubalen da gwamnatocin baya suka gaza shawo kansu. Ya kuma ce, fannin kamfanoni masu zaman kansu sun yaba da ci-gaban da ake samu, sannan gwamnatin ta duƙufa wajen tabbatar da ci-gaban tattalin ya amfani talakawan Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply