Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Mazauna yankunan da ke fama da ƙalubalen tsaro sun ce fitina ce a hankali ta zama haka. Zallawa da ke midibeliya sun ce a’a ƙabilanci ne!
Ni kai na ina da fayafayan bidiyo inda mazauna yankunan da ke fama da ƙalubalen tsaro ke bayyana labarin yadda lamuran su ka fara a hankali har su ka zama fitinar zubar da jini da sace mutane don karɓar kuɗin fansa. Ko kwanan nan a farmakin Kauran Namoda, mazauna yankin da a ka tattauna da su, sun koma ne ga neman taimakon Allah baya ga bukatar hukumomi su kawo mu su ɗauki don ceton rayuwa da dakiyoyinsu. Ko mutum daya ba wanda ya kawo batun ƙabilanci ko wani abu na makirci irin wanda wasu tsiraru ke yayatawa a soshiyal midiya.
Mun san daidai lokacin da mutane na gaskiya ke ba da labarin yadda lamuran ke faruwa da neman mafita, su kuma ‘yan kwangilar AIFOB da Midibelawa sun hau soshiyal midiya su na yayata cewa ƙabilanci ne ya kawo fitinar! To ƙabilanci tsakanin waye da waye kenan? Al’umma sun ce ga abun da ya ke damunsu kuma gwamnati da jami’an tsaro na bayanin matakan yaƙi da ‘yan ta’adda amma wasu da ke birane da ƙauyukan da ko kaza ba a taba sacewa ba na rawar banjo su kurɓa kayan maye su na cewa a’a ai ƙabilanci ne!
Kai akwai masu makirci da ke cewa ‘yan ta’addan wai na karisa jihadin Shehu Mujaddadi ne! haƙiƙa duk mai fadar wannan ba wata doguwar tambaya mutanen ne da ke yaƙi da addinin da rinajyen Hausawa ke kai. Ai ba wani wanda ba Musulmi ba da su ke zagi a duk tarihin shekara 200 ko ma har miliyan 50 da su ke magana sai Musulmi kaɗai. Wannan na nuna hatta addinin Kiristancin sun juya ma sa akala zuwa muradunsu na son zuciya.
Miyagun nan da wasu ma ba ma a Nijeriya su ke da zama ba na rura wutar yaƙi da zummar gaba ɗaya Arewa ta kama da wuta bal-bal don cimmawa iyayen gidansu Kadamusawa buri da samawa ‘yan awaren Biyafara hanya bulus ta wargaza ƙasar yayin da ‘yan ƙauyukansu na Midibelawa za su haɗe da su ko su cika muradin zama ba da sunan Arewa na Hausawa ba. A wajen mutanen, can cikin zuciyarsu a ɓoye sunan “AREWA” na nufin Musulunci ne. Kawai mugun nufin mutanen nan na neman kawo zaman doya da manja tsakanin Musulmi da Kirista.
A baya-bayan nan da Zallawa su ka ga sharrin da su ke shukawa ya ki kawo wutar da su ke buƙata sai su ka koma tallata wasu ‘yan siyasa kuma abun mamaki ba cikakken Bahaushe kuma ba ma Musulmi a ciki. Dama karya da yaudara na da iyaka musamman a majalisar masu nazari. Mutanen nan ba su da wata alaƙa da ta wuce kiyayya ga Hausawa.
Zallawa na kara fito da ajanda yayin da sabuwar ƙungiyar iƙirarin ‘yan kasa Hausa-Kiristan ta bayyana. Na yi bayani a baya sau curin masaki cewa ‘yan ƙungiyar iƙirarin Hausa Zalla na da muradin karfafa ajandar addininsu ne a tsakanin Hausawa Musulmi mafiya rinjaye. Na kawo mu ku yadda su ke ƙorafin wai a na yunƙurin Musuluntar da Arewa da ma danne hakkin mabiya addinin kirista. Yayin da Midibelawa su ka kai kara har wajen Turam, kungiyoyin ikirarin Hausa-Kiristan na fakewa da ƙabilanci ta hanyar saka rigar Hausawa don neman rage tasirin Musulunci. Ba ma sai na maimaita yadda Zallawa ke zagi mai maiko ga Shehu Mujaddadi, manyan sarakuna da malaman Musulunci ba, amma ko babban mutum daya wanda ba musulmi ba bai taɓa samun kason zagin ba.
Mun tuna yadda ƙungiyar Hausa-Kiristan ta HACDI HAUSA CHRISTIAN DEVELOPMENT INITIATIVE ƙarƙashin Farfesa Daniel Danladi Musa ta yi taro a Kano da naɗa Rabaran Shu’aibu Bargi a matsayin sarkin Hausawa mabiya addinin kirista na Kano da nuna hakan shi ne Bahaushe Ya Mulki Kansa. Gaskiyar magana ba wanda ya hana kowa yin addininsa a Arewa amma ba za a zura ido wasu na saka rigar Hausawa don yayata fitina da zummar ƙarfafa wani addini ba. Maimakon cusa Hausa ko kabila a lamarin addini, kawai su fito fili su ƙaddamar da ƙungiyoyinsu na addini. Wani Bahaushe ya mulki kansa duk yaudara ce ta ɓullo da wani makirci ta bayan gida.
Sarautar Hausawa Kirista na nufin ai mai martaba sarkin Kano na sarautar Musulmi ne don haka Zallawa ke manna kabilanci wai Fulani ya ke jagoranta don haka kenan ga Rabaran Bargi na Hausawa! Haka ne ma na, tun da bisa rinjaye da sai mu ga Zallawa sun naɗa sarkin Hausawa musulmi gabanin yin nasu na Kirista. Shin wannan ai ya fito ma na da inda addinin Zallawa ya dosa.
Duk lokacin da a ka yi irin wannan haskawa wasu marar sa basira sai su wurgo hoton shugaban Fulani-Kiristan a matsayin martani. Me shugaban Fulbe Kiristan Rabaran Buba Aliyu ya yi ko wa ya zaga? ko wace sarauta ya nada a Filato inda ya ke zaune? Wa ya ji ya na maganar akwai wani bambanci na kabila a zamantakewar al’ummar Arewa? Gaskiya ba wata shaida ta hakan.
Abun da ya bayyana shi ne ajanda ce kawai ta manna kabila jikin addini don addini na kowa ne kuma ya hana kabilanci sam. Hatta wadannan Kiristocin masu manna Hausa a tafiyarsu ba su da hurumin yin hakan daga Baibul don addinin ba su kaɗai su ka shige shi ba a nan Arewa. Shin akwai wanda ya isa a nan Arewa ya ayyana Hausa-Muslim? Ba ma Arewa kaɗai ba duk duniya akwai wata ƙungiya ta Hausawa-musulmi? Amsa-Babu ko a mafarki. Musulunci na kowa ne daga bangon gabar zuwa bangon yamma na duniya. A mugun kamfen na makirci da Zallawa ke yi ne kaɗai za ka ji su na cewa malamai ko limaman Fulani ko wani shakiyanci irin wannan. Kowa ya gane su waye ke irin wannan salon a magana ‘yan angulu da kan zabo ne kuma tun asuba mun haska su.
Shawara a nan ga duk mabiya addinin Kirista masu iƙirarin Hausa zalla ko su Hausawa ne su fito fili su yi addininsu don ba mahaluƙin da zai hana su saboda tsarin mulki ya ba wa duk dan Nijeriya hurumin yin addini amma bai ba wa kowa hurumin fakewa da ƙabilanci don ruruta fitinar addini ba.
Masu cusa ƙabilanci ƙarfi da yaji a ta’addancin daji sun ɗauko kwangila mai wuyar sayarwa. Ginshikan tallar kwangilar shirga karya, danna ashar da bijirewa umurnin Allah
Haƙiƙa akwai waɗanda su ka fara biyewa Zallawa ‘yan kwangilar cusa ƙabilanci a dalilan ta’addancin daji, amma su ka kauce don yadda tafiyar ta zama lallai sai an haɗa da murɗe wuyan tarihi rana tsaka, zunduma ashar ta uwa ta uba ga wanda bai yi laifin komai ba da kuma bijirewa umurnin Allah ta nuna wai an yaudari Hausawa da addinin Musulunci. Ba mai cimma wadannan turakun farafaganda sai gafalalle mai adawa da haɗin kan Hausawa, addinin gaskiya da Arewa.
Zallawa da kan yi zagi da yin duk nau’i na cin mutunci ga ko ma waye da bai yarda da sabgarsu ba, a lokaci guda ba sa kaunar a nusar da su hanyar gaskiya don dama su a wajensu kawai ko ka ji tsoronsu don sharrinsu ko ka koma gefe ka kyale su su kona ƙasar don ba su da asara. Yadda su kan yi caa da bakar magana, yarfe da yayata labarun karya na tabbatar da sun yi nisan da sai Allah ya yi mu su kwab ɗaya irin na Fir’auna kafin su gane rariya su ka kifa ba laima ba.
Hatta a nan soshiyal midiya akasarin Zallawa ba su da wata asara don an mayar mu su martani da ko ma menene don a ɓoye su ke fesa gubarsu ba sunan gaskiya ba hoto ba adireshi. Taron tsuntsiya ne ba shara ne don ba amfanin kula kusan kashi 99.9% na Zallawa saboda a ɓoye su ke ruff a salula. Don haka ai zai zama wauta wani ma ya tsaya ya na kokonton makircin waɗanda ke boye amma su na yayata kalaman haddasa yakin basasa a tsakanin al’ummar Arewa.
KAMMALAWA
Mu dai kawai mu kan yi bayanai ne don haskawa jama’a kar su fada tarkon yaudarar Zallawa don duk duniya ba makiya Hausawa irinsu kuma babban dalilin kiyayyarsu ga Hausawa shi ne yadda Hausawa ke bin addinin Musulunci tsantsa ba sakarci ba rawar banjo ba bori ba tsafi ga shi kuma su na zaune lafiya mabiya addinin Kirista. Wallahi duk mai bin Allah SWT da koyarwar Manzon Allah ba zai bi hanyar Zallawa ba. Mutanen nan ba ma bukatar kafirtasu da su ke ƙorafi don dama wanda bai yi alwala ba ai ba za ka yi ma sa tayin sallah ba. In sun yi ganganci zai zama sun zo duniya a da kafar hagu kuma za su koma a kafar hagun wato ba riba ba tasiri kenan. Bin AIFOB da muradun Midibelawa da su ke yi kamar neman wanda ya fi ɓacewa hanyar gaskiya ne daga mai bautawa wanin Allah da har ranar alkiyama ba zai amsa ma sa ba.
Duk al’ummar Arewa daga kowane addini su riƙa takatsantsan da duk wanda ke da mummunar manufa kawo fitina wacce haƙiƙa in an bari ta tashi to gaskiya motar kasha gobara ba za ta iya kashe wutar ba. Allah ya sauwake.
