Gwamna Raɗɗa ya sauke shugaban KTTV Katsina daga muƙaminsa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa ya amince cikin gaggawa da sallamar Janaral Manaja na gidan Talabijin KTTV malam Abba Zayyan daga muƙamin sa nan take

Wata sanarwa da ta fito daga babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar, Malam Kaula Muhammad ya fitar ya ce tsohon manajan ƙasa tafiya da wata manufar gwamna Raɗɗa na tsarin gina makoma duk da ɗinbin kuɗi da gwamnati ta zuba a gidan Talabijin domin sake mata fasali tayi fice a ƙasa da duniya baki ɗaya.

Gwamna yace, gwamnatin sa ta samar da na’urori na zamani,ta gyara da ɗaukaka gine gine da bada cikakken goyon baya domin zamanantar da KTTV da za ta iya fuskantar kowace ƙalubale da kuma ɗaukaka martabar Katsina.

Ya nuna takaicin sa duk da ƙoƙarin da gwamnatin sa tayi na ɗaukaka darajar gidan talabijin sai gashi bata gaba bata baya.

Dikko Raɗɗa sai ya umarci mafi girma a muƙami a KTTV da ya ja ragamar shugabancin gidan talabijin kafin naɗa sabon Janaral Manaja.

By ukarofi

Leave a Reply