Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta samu wani babban nasara bayan ta ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kama waɗanda ake zargi uku, bayan wani aikin tsaro da aka gudanar a Dakingari, ƙaramar hukumar Suru.
Aikin ya biyo bayan sahihan bayanai cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen Dolen Kwandage, sun yi garkuwa da mazauna uku, wato Samaila Abubakar, mai shekara 35, Dayyaba Muhammadu, mai shekara 32, da Balki Hakimi, mai shekara 31.
Nan take, jami’an ‘yan sanda, tare da haɗin gwiwar ‘yan banga na gida, suka tashi zuwa wurin, suka bi sawun maharan. Arangamar da ta biyo baya ta tilasta masu garkuwa su bar mutanen da suka kama, wanda ya kai ga ceto sabbin mutane uku da aka yi garkuwa da su, da wasu mata biyu, Moe Muddaha, mai shekara 50, da Hadiza Bello, mai shekara 30, duk daga Kauyen Yarma, ƙaramar hukumar Suru, waɗanda aka riƙe a baya.
Dukkan mutane biyar an ceto su ba tare da wani rauni ba, an kai su babban asibitin Dakingari domin a duba lafiyarsu, daga bisani aka miƙa su ga iyalansu.
Aikin ya kuma kai ga kama waɗanda ake zargi uku: Umaru Janyo, mai shekara 49, da Bube Kwaire, mai shekara 28, duk daga Kauyen Bendu, da Muhammadu Gyade, mai shekara 22, daga Kauyen Tindifai. Sauran ‘yan ƙungiyar sun tsere da raunukan harbin bindiga da ake zargi. An ƙwato abubuwa kamar haka: babur Haojue guda daya ba tare da lamba ba, kudi Naira 308,000, sarka guda ɗaya, da jarkar mai guda daya.
Rundunar ta ƙara tsaurara sintiri da sa ido a yankin, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama sauran ‘yan kungiyar da suka tsere don a hukunta duk waɗanda ke da hannu.
Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Umar M. Hadejia, ya yaba wa jami’an da ‘yan banga na gida saboda saurin amsawa, jarumtaka da haɗin kai mai kyau. Ya sake jaddada kudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi, da tarwatsa hanyoyin aikata laifuka, da tabbatar da cewa masu aikata manyan laifuka ana hukunta su. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai akan lokaci ga hukumomin tsaro don ƙarfafa tsaron al’umma.
