NiMet ta yi hasashen hazo da hadari na kwana uku a sassan Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar da yanayi ta Ƙasa NiMet, ta fitar da rahoton hasashen yanayi a sassan Nijeriya, inda ta ce ana sa ran samun hazo tare da hadari daga ranar Litinin zuwa Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026. NiMet ta bayyana haka ne a wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026.

Hukumar ta yi hasashen samun hazo mai ɗauke da ƙura a sassan jihohin Arewa maso Yamma bakwai da suka haɗa da Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da Sakkwato a ranar Litinin. Ta ce, ana sa ran samun hasken rana na tsawon kwanaki ukun a sassan Arewa maso Gabas.

Haka kuma, ta yi hasashen samun matsakaicin hasken rana da hadari mai ɗauke da yayyafi a Arewa ta Tsakiya. Jihohin da hakan ya shafa sun haɗa da Kogi, Kwara, Benuwai, Abuja da Nasarawa.

A sassan Kudu, NiMet ta yi hasashen samun hadari da hasken rana da kuma yiwuwar tsawa da yayyafi a safiya. Daga bisani, ta ce ana sa ran samun yayyafi da tsawa a sassan jihohin Abia, Imo, Anambra, Enugu, Ebonyi, Ogun, Ondo da Legas. Sauran jihohin sun haɗa da Oyo, Osun, Edo, Delta, Bayelsa, Ribas Kuros-Riba da Akwa Ibom.

A ranar Talata, NiMet ta bayyana cewa, a arewacin ƙasar za a sami hasken rana ɗauke da halayen hazo da kuma tsawa da yayyafi a kudancin Jihar Taraba. Ta ce, za a samun hasken rana da hazo da ɓurɓushin hadari a Arewa ta Tsakiya.

A kudu, ana sa ran hadari da hasken rana akai-akai tare da yiwuwar tsawa da yayyafi a safiya. Kazalika a Laraba, NiMet ta bayyana sassan jihohin Anambra, Ebonyi, Abia, Kuros-Riba, Akwa Ibom, Ribas da Bayelsa a matsayin wurare da za a yi ruwan safe.

Akan haka ta shawarci al’umma da su kasance masu amfani da matakan kulawa musamman kan kiwon lafiya da ƙaurace wa lamuran da ka iya haddasa gobara a yankunansu.

By Babaji

Leave a Reply