Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Taron yaƙin neman zaɓen APC da aka kammala a shiyyar Funtua an bayyana shi a matsayin alamar nasarar jam’iyyar a babban zaɓen 2027.
Da yake bayani kan taron a Matazu, ɗan takarar kujerar majalisar wakilai Hamza Suleiman Faskari ya bayyana cewa taron ya jawo ɗimbin jama’a da aka gudanar cikin lumana da tsari a dukkan ƙananan hukumomi 11 na shiyar Funtua.
Faskari, ɗan takarar APC na kujerar Ƙanƙara, Faskari da Sabuwa, ya ce magoya baya daga kowane ɓangare — mata, matasa, manoma, ‘yan kasuwa, ƙwararru da ɗalibai — sun fito ƙwansu da kwarkwata don halartar tarukan kamfen na jam’iyyar APC a ƙananan hukumomi 11 da ke shiyar.
A cewarsa”Abin da muka gani ya wuce siyasa. Tarbar da aka yi mana tun daga Funtua, Faskari, Bakori, Danja, Malumfashi, Kankara da Dandume, ta nuna sarai cewa Katsina ta ci gaba da zama jihar APC.
Gwamna Raɗɗa ya yi amfani da taron don ƙaddamar da ayyukan hanyoyin karkara, asibitocin da aka gyara, ajujuwan makaranta da aka sabunta, tallafin noma, tallafin kuɗi ga mata ‘yan kasuwa, kayan aiki ga ƙwararrun sana’o’i da kayan noma ga manoma.
Ya kuma gana da sarakuna, shugabannin addini, ‘yan kasuwa da masu kula da rumfunan zaɓe don sauraron ƙorafe-ƙorafen su.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta cika alƙawuran zaɓe a dukkan mazaɓu 361, kuma ta ci gaba da aiwatar da ƙarin ayyuka bisa buƙatun al’umma.
A matsayinsa na shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu / Dikko a Katsina, ya buƙaci ya’yan jam’iyyar da su haɗa kai, su sulhunta bambance-bambance tare da ƙara himma daga rumfunan zaɓe.
Ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga tsaro, hanyoyi, ilimi, lafiya da samar da ayyukan yi, tare da kira ga masu zaɓe da su yi wa Shugaba Bola Tinubu da dukkan ‘yan takarar APC ruwan ƙuri’u a 2027.
Ana sa ran tawagar za ta koma shiyyoyin Daura da Katsina a makonni masu zuwa.
