Messi ya zama ɗan wasan MLS na farko da ya lashe kyautar mafi yawan ƙwallaye sau biyu a jere

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Zakaran ɗan ƙwallon ƙafar duniya Lionel Andres Messi, ya sake lashe kyautar 2026 MLS Golden Boot, wato ta ɗan wasa mai mafi yawan zura ƙwallo a gasar, wanda ya sa ya zama ɗan wasan Major League Soccer na farko a tarihi da ya lashe kyautar sau biyu a jere.

Ɗan wasan tsakiyar na Inter Miami ya kammala kakar wasan ne da zura ƙwallo 26 a raga, wanda ya ba shi damar doke mai gogayya da shi, Peter Musa na FC Dallas da ƙwallo huɗu.

Wannan ya nuna yadda ɗan wasan mai shekara 39 yake cigaba da mamaya a harkar ƙwallon ƙafa, bayan samun na farkon a 2025 a lokacin da ya zura ƙwallo 29 a kakar mai wasanni 31.

Wannan nasarar karya tarihin ta samu ne a ranar buga wasannin ƙarshe na gasar bayan Inter Miami ta yi 3 da 3 da ƙungiyar Charlotte FC. Duk da cewa Messi bai zura ƙwallo ko guda ba a wasan, ya taimaka an ci biyu daga bugun kusurwa.

Haka kuma, ɗan Ajantinan ya taimaka an zura ƙwallo 17, wanda ya kai jimillar adadin waɗanda ya taimaka aka ci zuwa 43 a gasar, lamarin da ya aa ya zama ɗan wasan MLS na farko ya bayar da gudumawar aka zura aƙalla ƙwallo 40 a kakar wasa biyu a jere.

By Babaji

Leave a Reply