Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta sanar da kama mutane biyar da ake zargi da sana’ar damfara tare da gano motoci biyu, katunan zama dan ƙasa da katunan tantance asusun mutane waɗanda dukkan su na jabu ne da kuɗi Naira miliyan biyu da kuma wayoyin hannu da ake zargi suna amfani da su wajen aikata hada hadar banki ta hanyar damfara.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanarwar haka,yace kamen ya biyo bayan takardar koke da wani mai suna Aminu Nasiru Dan Rimi a shigar a ofishin kwamishinan ‘yan sanda inda ya bayyana ɓacewar kuɗin sa Naira miliyan 10 a hannun Ahmed Abdulkarim ɗan shekara 23.
Sadiq ya bayyana cewa nan take yan sanda suka fara bincike da ta kai su da kama wanda ake zargi Ahmed Abdulkarim ya kuma tabbatar da amsar wannan kuɗi daga hunnun wanda ke ƙara.
Ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa da shi da Aminu Nasiru Dan Rimi wanda ya yi koke dukkan su yan damfara ne kuma wannan Naira miliyan 10 da ake zargi ya gudu da ita kuɗaɗen damfara da suka samu shi da Dan Rimi ne.
Haka kuma bincike ya kai ‘yan sanda da kama wasu abokan san’ar su Abdulkarim Abdullahi da Mustapha Ayuba waɗanda suka mallaki asusun bankuna guda shida kowanne.
DSP Abubakar Sadiq ya ƙara da cewa bincike ya kai jami’an ‘yan sanda da kama mataimakin manajan Fahad Ahmad na otel da zaune suna aikata hada hada su na damfara.
Ana zargin manajan da canzawa waɗanda ake zargi ɗakunan su domin kauce wa jami’an tsaro.
‘Yan sanda sun kuma kama mutane biyu Sefullahi Idris da Faruq Bala da zargin taimakawa yan damfarar da da samun katunan shaidar zama ɗan kasa (BVN) da na tantance asusun mutane (NIN) na jabu.
Kayayyakin da ‘yan sanda suka samu tare da yan damfarar sun haɗa da mota ƙirar Peugoat 206 da Mota ƙirar Marsandi C 300 da wayar hannu guda huɗu, jabun BVN guda tara, jabun NIN 10, katin fitar da kudi guda tara,SIM card na layuka daban daban guda 14 da kudi a ƙasa Naira miliyan biyu.
Harwala yau jami’an ‘yan sanda a cewar sanarwar sun sahalewa rufe asusun waɗanda ake zargi tare da fitar da Naira miliyan 22 daga asusun ‘yan damfarar.
Sun kuma gano Aminu Nasiru Dan Rimi wanda ya shigar da koke da Surajo Sani Muhammad waɗanda ake nema ruwa a Jallo matsayin manyan jagororin ‘yan damfarar.
Yanzu haka ‘yan sanda sun shiga farautar waɗannan Jagorori da yan Sanda suka bayyana su a matsayin jagororin ‘yan danfarar.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Fage ya yaba wa ‘yan sanda kan yadda suka nuna ƙwazo da ƙwarewa, ya tabbatar wa al’ummar Katsina cewa ba za su gajiya ba sai sun kawar da irin waɗannan ɓatagari, ya kuma gargaɗi masu gidajen Otel a jihar su guji bada mafaka ga irin waɗannan ɓatagari.
