‘Ba za ka yi nadamar zaɓin zaman lafiya ba’ – Tinubu ga Fubara a gangamin Ribas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba da rawar da masu zaɓen Jihar Ribas suka taka a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da ya ba shi nasara, yayin da ya sake neman goyon bayansu ga zaɓen da za a yi a ranar 16 ga Junairu, 2027 domin ƙarfafa wa ribar da aka samu a ƙarƙashin gwamnatinsa.

Shugaban Nijeriyar ya yi wannan magiya ne a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓensa da aka gudanar a filin wasa na Adokiye Amiesimaka Stadium da ke Fatakwal, inda ya yaba wa dandazon jama’ar da suka halarta domin nuna goyon bayansu a gare shi, sannan ya yaba wa wa sulhun siyasar da aka samu tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da wanda ya gada, Ministan Abuja Nyesom Wike.

Waɗannan kalamai na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sanya hannun Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga da aka fitar a ranar 7 ga Nuwamba, 2026. Tafiyar Rainbow Coalition ƙarƙashin jagorancin Wike ce ta shirya taron, wanda ya haɗa jagororin siyasa da magoya baya daga sassan jihar Ribas.

Shugaba Tinubu ya ce Gwamna Fubara ya nuna dattako, fahimta da girmama shigar manyan ‘yan siyasa wajen warware rikicin da ke tsakaninsa da Wike. “..Fubara ba za ka yi nadamar abin da ka yi ba muddin dukkan mu muna raye,” inji Shugaban.

Da yake jawabi kan tattalin arziƙi, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gyare-gyaren gwamnatinsa suna ƙoƙarin ɗora ƙasar a hanyoyin samun nasarori da ci-gaba mai ɗorewa. A cewarsa, Gwamnatin Tarayya tana ƙoƙarin magance matsalolin nauye-nauyen da ta gada daga gwamnatocin baya, ciki har da bashin kuɗaɗen fansho da giratuti, yana mai cewa za su tabbatar da ƙarin wasu iyalai sun amfana daga halin farfaɗowar tattalin arziƙi.

Shugaban Nijeriyar ya kuma yi iƙirarin cewa sun biya basusukan fansho da albashin ma’aikata da aka riƙe na ‘yan jihohi 27 daga guda 36, inda ya ce a yanzu masu amfana suna samun tabbacin biyan haƙƙoƙinsu a kowane wata.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya yi kira ga jagororin siyasa da magoya baya a Jihar Ribas da sassan Kudu maso Kudu da su goyi bayan sake zaɓar Tinubu, inda ya bayar da misali da ƙoƙarin gwamnatin da hidimarta ga shiyyar a matsayin dalilan hakan. Ya bayyana cewa, a yanzu rarar kuɗin ajiyar Nijeriya a ƙasashen waje ya kai Dala biliyan 60 daga Dala biliyan 3.9 a tsawon shekaru uku na gwamnatinsu.

By Babaji

Leave a Reply