
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan tawagar Flamingos na Nijeriya sun yi nasarar lashe Kofin Duniya na FIFA na Mata ‘yan ƙasa da shekara 17 na 2026 a karon farko a tarihi bayan da suka doke Japan da ci 2 da 1 a wasan ƙarshe da aka buga a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026.
Wannan nasara ta kafa sabuwar tarihin ga harkar ƙwallon ƙafar Nijeriya da kuma Afirka. Flamingos ta zama tawagar Afirka ta farko da ta taɓa lashe kofin, wanda ya samu daga ƙwallayen da Awawu Bashiru da Oluebube Umejiaku suka zura.
Awawu, wadda ‘yar wasan tsakiya ce, ita ta fara zura ƙwallo a wasan ta hannun Mary Dunstan a minti na 39 wanda ya bai wa Nijeriya damar jan ragamar wasan gabanin tafiya hutun rabin lokaci. Nijeriya ta ƙara ƙwallo ta biyu ne a raga bayan mintina biyu da koma wa hutun rabin lokaci, a lokacin da ta Umejiaku ta samu ƙwallo ta hannun Esther Stephen.
Ana haka ne Japan ta samu damar farfaɗowa a wasan ne a minti na 80 ta ‘yar wasa Fuki Ito a lokacin da Anri Ito ta gara mata ball, lamarin da ya mayar da wasan 2 da 1. Wannan ƙwallo ya sa Japan ta samu ƙwarin-gwiwar cigaba da matsa wa ‘yan Flamingos wajen ganin sun farke har na tsawon minti 15, amma ba su samu dama ba daga ‘ya’yan Nijeriyar.
Gabanin zuwa Moroko, inda aka gudanar da gasar, Flamingos ta lashe kofin 2026 WAFU-B U-17 Girls Cup a ƙasar Ivory coast bayan samun nasara a wasanni biyar, inda ta zura ƙwallo 17 a sanadiyyar haka, yayin da aka zura mata ɗaya kacal.
