2027: Ya kamata Atiku ya haƙura ya mara wa Obi baya – Kwankwaso

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya gargaɗi tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan yunƙurin neman kujerar shugaban ƙasa daga Arewa a zaɓen 2027, yana mai cewa ya kamata Kudu ta samar da shugaban ƙasa na gaba.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin ganawa da ’yan jarida a gidansa da ke Kano, inda ya ce bai kamata a karya tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu ba.

Ya buƙaci Atiku da ya ajiye burinsa na takarar shugaban ƙasa tare da mara wa Peter Obi baya, domin a cewarsa, lokacin Kudu ne na jagorantar ƙasar kafin mulki ya koma Arewa.

Tsohon Gwamnan na Kano ya ce ya sadaukar da burinsa na shugabancin ƙasa domin goyon bayan Obi, saboda suna da manufa da akidu iri ɗaya.

Ya ƙara da cewa barin wani ɗan Arewa ya fito takara a 2027 zai iya haifar da ruɗani da rashin jituwa a siyasar ƙasar, duk da cewa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya bai tanadi tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin yankunan ƙasar ba.

By ukarofi

Leave a Reply