An ƙaddamar da jami’an tsare-tsaren ƙungiyar WOPU 44 a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An ƙaddamar da shugabannin tsare-tsaren ƙungiyar ma’aikata masu haɗa kai da al’umma, wato Working People United (WOPU), ƙarƙashin jagorancin Kwamared Hashim A. Sale, wanda shi ne babban jami’in ƙungiyar na Kano.

Kwamared Hashim na ɗaya daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabi a taron da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata, a ɗakin karatu na tunawa da Marigayi Murtala Muhammad da ke birnin Kano, Nijeriya.

Kwamared Hashim, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sasanta Ma’aikata ta JNC reshen Kano, ya bayyana cewa babu wata ƙasa da za ta zauna lafiya ba tare da ma’aikata ba. Ya ce ma’aikata su ne ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban al’umma a ko’ina cikin duniya.

Ya ƙara da cewa an kafa ƙungiyar ne domin zaɓar shugabanni na gari waɗanda za su jagoranci ayyukan ci gaba a Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Shi ma Kwamared Abdullahi Muhammad Gwarzo, Mataimakin Shugaban ƙungiyar Ma’aikatan ƙananan Hukumomi ta NULGE mai kula da shiyyar Arewa, a nasa jawabin, ya ce Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya cancanci yabo saboda wasu muhimman abubuwa da yake yi wa ma’aikata.

Ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da suka cancanci yabo akwai ba wa ma’aikata ƙarin girma, biyan albashi a kan lokaci, da kuma kula da sauran haƙƙoƙinsu da walwalarsu a kowane lokaci. Ya ce waɗannan matakai abin yabawa ne ga gwamnatin jihar Kano.

Kwamared Tajiddin Bashir Baba, wanda shi ne Shugaban ƙungiyar Ma’aikatan Manoma kuma Mai Unguwar Yakasai, ya bayyana cewa tsawon shekaru 30 suna neman a riƙa biyan ma’aikatan gona wani alawus na musamman sakamakon ƙarin lokutan aiki da suke yi, amma ba su samu wannan dama ba a baya.

Ya yi fatan gwamnatin Abba za ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin an samu ci gaba mai ma’ana wanda zai dore a Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Tun da farko, a nasa jawabin, Shugabar Ma’aikata, Bilkisu Mai Mota, ta bayyana muhimmancin ma’aikata da yadda gwamnatin Kano ke kula da su da sauran al’umma, bisa la’akari da irin rawar da suke takawa wajen kawo ci gaban Kano da ƙasa baki ɗaya.

Haka kuma, Kwamared Bala Sani, shugaban ƙungiyar a Madobi, da Kwamared Usman Mani Karmami na Gabasawa, na daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin Kano da suka bayyana gamsuwarsu da tafiyar ƙungiyar WOPU.

By ukarofi

Leave a Reply