Matasan APC a Yobe sun gudanar da gangamin nuna goyon baya ga Tinubu

Spread the love

Daga SANI GAZAS CHINADE Damaturu

Matasan jam’iyyar APC a jihar Yobe sun gudanar da wani gangami don nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da ‘yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress gabanin babban zaɓen 2027.

Gangamin, wanda aka gudanar a Damaturu ranar Asabar, matasa ne ƙarƙashin inuwar ƙungiyar Tinubu Must Go Again suka shirya shi.

Sakataren gwamnatin jihar Yobe, Dr Mohammed Goje; shugaban ƙungiyar na jiha, Farfesa Sherif Sheriff Almuhajir; Hassan Shettima; Bature Goniri; da shugabannin matasa daga sassan jihar ne suka halarci taron.

Masu halartar taron sun yi alƙawarin bayar da goyon bayansu ga ƙudurin sake zaɓen Tinubu da ‘yan takarar jam’iyyar APC da ke neman muƙamai a matakin tarayya, jiha da kuma ƙananan hukumomi.

Haka zalika, sun nuna goyon bayansu ga ƙoƙarin gwamna Mai Mala Buni na ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a ɗaukacin jihar a zaɓen 2027.

Aminiya ta ruwaito cewa, gangamin na nuni da wani yunƙuri na gaggauta haɗa kai da ƙungiyar ta yi gabanin babban zaɓen 2027, yayin da ayyukan siyasa da yaƙin neman goyon baya ke fara ɗaukar zafi.

By ukarofi

Leave a Reply