Rasha ta ƙaddamar da gagarumin farmaki kan Ukraine

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Yayin da ƙoƙarin diflomasiyya ke ci gaba da neman hanyar kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine, sabon farmakin da Moscow ta ƙaddamar kan cibiyoyin samar da wutar lantarki a Ukraine ya sake tayar da hankula, tare da ƙara nuna yadda har yanzu yaƙin ke ci gaba da jefa rayuwar fararen hula cikin mawuyacin hali.

A ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, Rasha ta ƙaddamar da wani gagarumin farmakin sama da ya haɗa da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa, inda aka kai hare-hare kan cibiyoyin samar da wutar lantarki da sauran muhimman wurare a Ukraine.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bayyana cewa Rasha ta harba jiragen yaƙi marasa matuƙa 289, makamai masu linzami na ballistic guda 17 da wasu makamai masu linzami masu bin dogon zango guda 59. Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun shafi wurare daban-daban, tun daga yankin Odesa da ke kudancin ƙasar zuwa yankin Rivne da ke yammacin Ukraine.

Kamfanin samar da wutar lantarki mai zaman kansa mafi girma a Ukraine, DTEK, ya bayyana cewa uku daga cikin cibiyoyinsa biyar na samar da wutar lantarki sun daina aiki sakamakon farmakin. Hukumomin ƙasar sun kuma tabbatar da cewa lalacewar cibiyoyin samar da wutar ta janyo katsewar wutar lantarki a babban birnin Kyiv da wasu yankuna shida.

A gefe guda kuma, Rasha ta zargi Ukraine da kai wani harin jirgin sama marar matuƙi kan wata babbar matatar mai da ke birnin Yaroslavl na Rasha, wanda ya haddasa gobara. Wannan sabon farmaki ya zo ne mako guda kafin lokacin da ake sa ran sake dawo da tattaunawar zaman lafiya da Amurka ke shiga tsakani.

Duk da ƙoƙarin da ake yi na samun mafita ta hanyar tattaunawa, sabon harin ya nuna cewa har yanzu akwai manyan ƙalubale a ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin da ya shafe kusan shekaru biyar yana gudana.

By ukarofi

Leave a Reply