
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Ƙolin Shari’a a Nijeriya (SCSN), ta naɗa Farfesa Ahmad Bello Dogarawa a matsayin sabon Sakatare Janar ɗinta biyo bayan rasuwar mai riƙe da muƙamin, Nafi’u Baba Ahmad a watan da ya gabata.
Shugaban SCSN, Farfesa Bashir Aliyu Umar ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ranar Asabar, 6 ga Nuwamba, 2026.
A cewar majalisar, an naɗa Dogarawa a muƙamin ne bisa ƙoƙarinsa wajen gudanar da harkokin jagoranci, yaɗa manufofi da ciyar da harkokin addinin Islama gaba musamman ta hanyar ɗaukar nauyi, kira ga muhimman al’amura, tattaunawa da shiga lamuran da suka shafi ƙasa.
Majalisar ta ce, Dogarawa Farfesa Lamuran Kuɗi ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), kuma masanin fiqhun musulunci, tattali a musulunce, harkar kuɗi mara ruwa, ci-gaban al’umma da fafutukar zaman lafiya a matakin ƙasa.
Akan haka ne ta yi kira ga al’umma, ƙungiyoyin musulunci, sarakunan gargajiya da ɗaukacin al’ummar musulmi da su ba wa farfesan goyon baya wajen sauke nauyin da aka ɗora masa. A ƙarshe, ta yi masa addu’ar Allah ya yi riƙo da hannunsa wajen sauke nauyin da kuma addu’ar Allah ya jiƙan wanda ya gada, wato marigayi Nafi’u Baba Ahmad.
