
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), tana sanar da al’umma kan wanzuwa shafukan kafar Facebook, guruf-guruf da wasu shafukan kafafen soshiyal mediya ke amfani da bajen hukumar, sunanta, ko wasu bayananta ba tare da sahalewa ba.
Don haka ta sanar da cewa ba ta da wani shafi na daban daga kafafen sadarwar da ta amince da su.
A wata sanarwa da Kakakin NAHCON, Shafi’i Sani Mohammed ya fitar, hukumar ta koka kan yadda wasu ke amfani da sunanta wajen yaɗa labaran da ba a tantance ba masu ruɗar da al’umma.
A saboda haka ta zayyano shafuka kamar haka a matsayin waɗannan ta aminta da su da rake yaɗa dukkan wani abin da ya shafe ta ta su:
- Official Website: https://nahcon.gov.ng
- Facebook: @nigeriahajjcom
- X (Twitter): @nigeriahajjcom
- Instagram: @nigeriahajjcom
- YouTube: youtube.com/@nahcon
Sannan, ta shawarci al’umma da su riƙa bin shafukan domin samun dukkan wani bayani ko labari da suke nema a wajenta tare da ƙaurace wa waɗanda ta bayyana a matsayin na bogi.
Kazalika, ta gargaɗi jama’a da su daina yaɗa labaran da ba a tantance su ba da sunanta, wanda ka iya zama ɓatanci a gare ta, tana mai kira da a riƙa yin ƙorafin (Reporting) dukkan wasu shafuka da ake zargin na bogi ne.
