Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta bayyana cewa asusun tallafin gaggawa na Naira biliyan 10 da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi a watan Yunin 2026, a lokacin da cutar Ebola ta ɓarke a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, ba domin yaƙi da Ebola kaɗai aka ware shi ba.
Hukumar ta ce, an ware kuɗaɗen ne domin ƙarfafa shirin tunkarar barazanar yaɗuwar cututtuka daban-daban a Nijeriya. Babban Daraktan hukumar, Dakta Jide Idris, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani kan tambayoyi game da yadda aka ware kuɗaɗen.
Batun ya ja hankalin jama’a ne bayan da Nijeriya ta tabbatar da samun mutum ɗaya da ya shigo da cutar Ebola daga wata ƙasa a watan Oktoba. Idris ya ce, an nemi kuɗaɗen ne domin inganta matakan kariya, shirin ko-ta-kwana, gano cututtuka tun da wuri, ɗaukar matakin gaggawa da farfaɗowa bayan aukuwar matsalar lafiya. Ya bayyana cewa tallafin ya shafi cututtukan da ke barazana ga lafiyar jama’a, ciki har da Ebola, zazzaɓin Lassa, kwalara, sanƙarau, cutar mashaƙo, wato Diphtheria, kyanda da kuma matsalar ƙwayoyin cuta da suka saɓa wa magungunan kashe ƙwayoyin cuta. Babban Daraktan ya kuma bayyana cewa an miƙa kuɗaɗen kai tsaye ga hukumar NCDC, ba ga Kwamitin Shugaban ƙasa kan Cutar Ebola ba, wanda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ke jagoranta.
Da yake fayyace batun, Idris ya ce, “Shin an miƙa kuɗin ga Kwamitin Shugaban ƙasa kan Cutar Ebola (PTF), wanda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa ke jagoranta? A’a. “An kafa kwamitin ne da farko domin daidaita yadda ƙasa za ta tunkari cutar. Amma naira biliyan 10 ɗin da ake magana a kai an miƙa su ne ga NCDC domin biyan buƙatun tsaron lafiyar al’umma da suka fi wannan faɗi.”
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda wasu ’yan siyasa ke haɗa adawa ta gaskiya da yaɗa bayanan ƙarya da kuma munanan zarge-zarge. A cewarsa, kare lafiyar al’umma wani muhimmin ɓangare ne na tsaron ƙasa, don haka bai kamata a mayar da shi rigimar siyasa ba. Ya ƙara da cewa, ya kamata ’yan siyasa da sauran masu sharhi kan al’amuran jama’a su guji yaɗa bayanan da ba su da tushe, musamman a lokacin da ake fuskantar barazanar annobar cuta, domin sahihan bayanai da amincewar jama’a suna da matuƙar muhimmanci a irin wannan yanayi.
Sai dai Idris ya ce tallafin naira biliyan 10 bai wadatar ba idan aka kwatanta shi da buƙatun Nijeriya na kare lafiyar al’umma daga cututtuka masu yaɗuwa. Ya bayyana cewa ƙasar na buƙatar kimanin naira biliyan 104.4 a duk shekara domin aiwatar da Tsarin Aiki na ƙasa kan Tsaron Lafiya, mai taken NAPHS 2.0. Ya ce shirin, wanda zai gudana daga shekarar 2025 zuwa 2029, zai lakume kimanin naira biliyan 522 cikin shekaru biyar.
A cewarsa, tallafin naira biliyan 10 da aka ware ya kai kusan kashi biyu cikin 100 na matsakaicin kuɗin da ake buƙata a shekara domin aiwatar da shirin. Ya ce bai dace a ɗauki wannan tallafi a matsayin kuɗi mai yawa ba, ba tare da la’akari da girman buƙatun ƙasar na kare lafiyar al’umma da kuma ayyukan da za a gudanar da kuɗaɗen ba. Idris ya ce, “Kuɗin aiwatar da shirin NAPHS 2.0 shi kaɗai ya kai kusan naira biliyan 522 cikin shekaru biyar. Wannan na nufin ana buƙatar matsakaicin naira biliyan 104.4 a duk shekara.
“Ko da yake ba dukkan ayyukan shirin ne NCDC ke ɗaukar nauyinsu ba, wannan adadi yana nuna irin jarin da ake buƙata domin kare ’yan Nijeriya daga barazanar cututtukan da ke shafar lafiyar jama’a. Haka kuma, idan aka kwatanta, naira biliyan 10 na wakiltar kusan kashi biyu cikin 100 na matsakaicin kuɗin da ake buƙata a shekara. Saboda haka, bai kamata a bayyana tallafin a matsayin kuɗi mai yawa ba tare da la’akari da girman buƙatun tsaron lafiyar ƙasa da ayyukan da aka ware shi domin tallafawa ba.”
Babban Daraktan ya kuma bayyana cewa kasafin kuɗin hukumar ya ƙaru daga naira biliyan huɗu a shekarar 2024 zuwa naira biliyan bakwai a shekarar 2025, yayin da kasafin kuɗin shekarar 2026 ya ware mata naira biliyan 22. Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta amince da wani tallafin gaggawa na naira biliyan biyar a shekarar 2025, kafin Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙarin naira biliyan 10 a watan Yunin 2026, lokacin da ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta zama barazanar da ta shafi duniya.
Duk da waɗannan ƙarin kuɗaɗe, Idris ya ce har yanzu akwai babban gibi tsakanin kuɗaɗen da ake da su da kuma waɗanda ake buƙata. Ya yi ƙaulin ƙiyasin Hukumar Sa Ido kan Shirin Ko-ta-kwana na Duniya (Global Preparedness Monitoring Board), wadda ta ce kowace ƙasa na buƙatar ware tsakanin dala ɗaya zuwa biyu ga kowane mutum a duk shekara domin samun ingantaccen shirin tunkarar annoba.
Ya ce idan aka yi la’akari da yawan al’ummar Nijeriya da ya kai kusan miliyan 240, ƙasar na buƙatar tsakanin dala miliyan 240 zuwa miliyan 480 a duk shekara. Idris ya jaddada cewa ci gaba da zuba kuɗaɗen gwamnati, na jihohi da na abokan hulɗa shi ne hanyar da za a bi domin rage wannan gibi.
