Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, na fama da gajiyar jiki sakamakon yawan ayyukan siyasa da tafiye-tafiyen da yake yi, a cewar tawagar yaƙin neman zaɓensa.
Mataimakin Kakakin Yaƙin Neman Zaɓen jam’iyyar, Sam Omale, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya yi watsi da fargabar da ake nunawa kan lafiyar tsohon gwamnan Jihar Anambra. Omale ya ce Obi na yawan zirga-zirga tsakanin wurare daban-daban domin halartar tarurrukan siyasa da sauran ayyukan jam’iyya, lamarin da ke hana shi samun isasshen lokacin hutawa.
Ya jaddada cewa ɗan takarar na cikin ƙoshin lafiya, kuma abin da yake fama da shi ba komai ba ne illa gajiyar jiki sakamakon yawan ayyukan da yake gudanarwa. Ya ce, “A wasu lokuta nakan yi mamakin inda yake samun ƙarfin da yake yi. Yau yana Landan, washegari kuma ka same shi a Enugu. Nakan yi mamakin yadda yake iya yin hakan. A ƙarshe gajiya tana kama mutum, domin shi ma ɗan Adam ne.”
Omale ya ƙara da cewa: “Yana cikin ƙoshin lafiya. Babu wata matsala da yake fama da ita. Gajiya ce kawai, kuma muna ƙoƙarin shawo kansa ya rage gudun ayyukansa tare da samun isasshen barci. Yana lafiya.”
Kakakin yaƙin neman zaɓen ya kuma bayyana cewa wannan gajiyar da Obi ke fama da ita ba za ta kawo cikas ga kamfen ɗin jam’iyyar da ake gudanarwa ba. Ya ce mambobin tawagarsa na ƙoƙarin shawo kansa ya rage ayyuka domin samun isasshen hutu.
Wannan bayani na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Obi ya soki Shugaban ƙasa Bola Tinubu kan yadda yake gudanar da mulki, inda ya nuna shakku kan ƙarfin jikinsa da kuma cancantarsa ta jagorantar Nijeriya.
A wani taron tattaunawa da jama’a da aka gudanar a Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi, Obi ya ƙalubalanci Tinubu da ya ziyarci jihar domin bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu, tare da fayyace yadda ta yi amfani da kuɗaɗen bashin da ta karɓa cikin shekaru uku da suka gabata. Tsohon gwamnan na Anambra ya kuma yi iƙirarin cewa Tinubu ba shi da ƙarfin jikin da zai zagaya ƙasar nan domin gudanar da yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
Obi ya ce, “Shugaba Tinubu ba shi da cancantar gudanar da mulkin Nijeriya. Ba shi da ƙarfin jikin da zai iya tafiyar da ƙasar nan. Ya tattara kayansa, ya koma gida ya huta.”
Ya kuma buƙaci mazauna Jihar Ebonyi da kada su goyi bayansa saboda ƙabilarsa ko yankin da ya fito, sai dai su yi la’akari da cancantarsa da kuma ƙwarewarsa ta jagorantar ƙasar. Ya ce,.“Kada wani ya raba kan mutanen Kudu maso Gabas. Ba na son mutanen Ebonyi su zaɓe ni saboda ni ɗan Kudu maso Gabas ne. Ba na son su zaɓe ni saboda ni ɗan ƙabilar Ibo ne.”
Ya ƙara da cewa, “Ya ku ’yan uwana, ina son ku zaɓe ni ne saboda na cancanci zama Shugaban ƙasar nan. Ina son ku zaɓe ni ne saboda ni ne ɗan takarar da ke kan gaba.”
Obi ya kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa Tinubu ba ya halartar wasu ayyukan yaƙin neman zaɓe, inda ya yi zargin cewa shugaban ƙasar ya shafe sama da kwanaki 260 a wajen Nijeriya, amma ya kasa ware kwanaki 36 domin zagaya ƙasar ya gana da jama’a. Ya ce, “Ina son Shugaba Tinubu ya zo Abakaliki ya bayyana wa jama’a abin da ya yi cikin shekaru uku da suka gabata. Ina son ya zo ya gaya muku abin da ya yi da kuɗaɗen bashin da yake karɓa a tsawon waɗannan shekaru uku.”
Obi ya ce, “Shugaba Tinubu ya shafe sama da kwanaki 260 a wajen Nijeriya, amma ya kasa ware kwanaki 36 domin zagaya ƙasar nan ya gaya wa jama’a abin da ya yi cikin shekaru ukun da suka gabata. Ba za mu yi haka ba.”
