El-Rufai ya umarci magoya bayansa su zaɓi ’yan takarar ADC a zaɓen 2027 yayin da yake a tsare

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya buƙaci magoya bayansa da su zaɓi ’yan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a dukkan matakai na zaɓen shekarar 2027.

Mataimakiyar Shugabar ADC ta shiyyar Arewa maso Yamma, Hafsat Baba, ce ta bayyana hakan yayin wani taron haɗin gwiwar ƙungiyoyin goyon bayan El-Rufai da aka gudanar a Jihar Kaduna.

Baba ta ce umarnin El-Rufai ya shafi zaɓen shugaban ƙasa, gwamna, Majalisar Tarayya da kuma Majalisar Dokokin Jiha a dukkan ƙananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna.

Ta ƙara da cewa an shirya taron ne domin haɗa ƙungiyoyin goyon bayan tsohon gwamnan wuri guda da kuma daidaita ayyukansu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Mataimakiyar shugabar ta shiyyar ta kuma bayyana cewa haɗakar ƙungiyoyin na shirin samar da rumbun bayanan magoya bayan El-Rufai a faɗin Jihar Kaduna, tare da ci gaba da gudanar da taruka akai-akai domin ƙarfafa harkokin wayar da kan jama’a da haɗa kan magoya baya.

Ta ce magoya bayan ADC sun kuduri aniyar ci gaba da kare manufofi da ayyukan da El-Rufai ya gada, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya da kuma ƙarfafa tattalin arzikin al’umma.

Haka kuma, ta nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a wasu sassan Jihar Kaduna, musamman Birnin Gwari, Giwa da Millennium City, inda ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Baba ta yi zargin cewa jami’an tsaro sun kama sama da magoya bayan El-Rufai 30 kimanin makonni biyu kafin taron, bisa yanayin da ta bayyana a matsayin wanda ke da shakku.

Ta buƙaci jami’an tsaro da su kasance masu adalci da rashin nuna bambanci, tare da gudanar da ayyukansu bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply