Buhari ya sayar da ɗanyen man da ba a haƙo ba, Tinubu na biyan bashin – Mutfwang

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya zargi gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da sayar da ɗanyen man fetur tun kafin a haƙo shi daga ƙasa, yana mai cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da biyan bashin da aka samu sakamakon wannan yarjejeniya.

Mutfwang ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na babban zaɓen 2027, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Rayfield, Jos.

Gwamnan ya ɗora alhakin wasu daga cikin matsalolin tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta gada a shekarar 2023 kan gwamnatin da ta gabata, yana mai cewa gwamnatin yanzu tana buƙatar lokaci domin sauye-sauyen da take aiwatarwa su fara haifar da sakamako.

A cewarsa, “ɗaya daga cikin matsalolin gwamnatin Buhari shi ne, sun kai wani mataki da suka rasa abin da za su yi, saboda haka suka sayar da ɗanyen manmu na nan gaba.

“An riga an sayar da ɗanyen man da ba mu ma haƙo daga ƙasa ba. A yau kuma muna biyan bashin wannan yarjejeniya. Don haka ba za mu yi tsammanin komai zai sauya cikin dare ɗaya ba.”

Mutfwang ya kuma bayyana tsarin tallafin man fetur da aka gudanar a lokacin gwamnatin da ta gabata a matsayin wata babbar damfara ta ƙasa, yana mai cewa gwamnati ta riƙa karɓar bashi domin biyan kuɗaɗen tallafin da ake iƙirarin bayarwa bisa takardun bogi.

Ya ce, “Lokacin da Shugaban ƙasa ya karɓi mulki, akwai wata babbar damfara da ke gudana a ƙasa, wato tallafin man fetur. Na kira shi damfara ne saboda muna karɓar bashi domin biyan mutanen da ke gabatar da takardun ƙarya. Ba su samar da wata dukiya ba, sai dai takardun ƙarya da suke amfani da su wajen karɓar kuɗaɗen tallafi.

“Ba za ka ci gaba da karɓar bashi kana bai wa ɓarayi kuɗi ba. Dole ne a dakatar da hakan a wani lokaci. Amma idan aka dakatar, akwai lokacin da za a biya farashin wannan mataki, kuma akwai lokacin murmurewa.”

Gwamnan ya ce cire tallafin man fetur ya taimaka wajen inganta samuwar mai a gidajen mai, duk da cewa farashinsa ya ci gaba da kasancewa mai tsada.

Ya bayyana cewa, “A yau, godiya ga Allah, mun warware wani ɓangare na matsalar. Yanzu ana samun man fetur. Mai yiwuwa ba shi da sauƙin farashi, amma ana samunsa.

“Mu da muke cikin wannan zamani, ko waɗanda shekarunsu suka ɗan girmi namu, za mu iya tuna lokacin da muke kwashe kwanaki a layin gidajen mai, amma duk da haka ba ma samun man yadda ya kamata. Amma yanzu mun samu nasarar magance wannan matsala.”

Haka kuma, Mutfwang ya kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Nijeriya ya haura dala biliyan 50.

Ya ce lokacin da Tinubu ya karɓi mulki a shekarar 2023, Nijeriya tana cikin mawuyacin hali ta fuskar tattalin arziki, inda ta kasa biyan wasu basussukan ƙasashen waje, sannan kamfanonin ƙasashen waje suka fuskanci matsala wajen mayar da kuɗaɗensu daga Nijeriya saboda ƙarancin dalar Amurka.

A cewarsa, wannan ne ya sa wasu kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje suka dakatar da zirga-zirgarsu zuwa Nijeriya, saboda ba sa iya samun dalar da za su mayar da kuɗaɗensu.

Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ta ragu zuwa sama da dala biliyan uku, daga sama da dala biliyan 40 da aka tara tsawon shekaru, amma yanzu ta haura dala biliyan 50.

Da yake magana kan matakan da gwamnatinsa ta ɗauka domin rage raɗaɗin matsin tattalin arziki a Filato, Mutfwang ya lissafa ƙaddamar da motocin sufuri na Tin City Metro, dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasa a cikin Jos, rage kuɗin makaranta da kashi 50 cikin 100 a manyan makarantun jihar, da kuma ƙara alawus ɗin ɗalibai da kashi 300 cikin 100.

Ya kuma ambaci Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND) a matsayin ɗaya daga cikin shirye-shiryen gwamnatin tarayya da ke taimaka wa ’yan asalin Filato da ke karatu a manyan makarantu.

Dangane da zaɓen 2027, gwamnan ya buƙaci ’yan Nijeriya su mara wa Shugaba Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓe, yana mai cewa ya kamata a riƙa yin sauyin mulki tsakanin Arewa da Kudu.

Ya ce, “Dole ne mu amince cewa ya kamata mulki ya riƙa sauyawa tsakanin Arewa da Kudu. Idan Arewa ta yi shekara takwas, waɗanda ba mu da wani abin nunawa a kansu, adalci ne a bar Kudu ta yi wasu shekaru takwas.

“Domin idan ba mu mutunta wannan tsarin rabon mulki ba, wata rana hakan zai iya haifar mana da matsala.”

Mutfwang ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta lashe zaɓe a Jihar Filato, inda ya buƙaci mambobin jam’iyyar su mayar da hankali kan wayar da kan jama’a da neman goyon baya tun daga tushe, tare da gudanar da kamfen cikin lumana da tattaunawa kan manufofi.

Tun da farko, Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gwamna Mutfwang da Piyo na 2027, Sir Joseph N. Ari, ya bayyana cewa kwamitin ya samu sanarwar goyon baya daga ƙungiyoyi 115 masu tallafa wa takara.

Ya kuma yi alƙawarin gudanar da kamfen bisa ladabi, haɗin kai da ɗaukar nauyin ayyukan da aka ɗora wa kowa.

Ari ya buƙaci mambobin jam’iyyar su fito ranar 14 ga Nuwamba, 2026, domin tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da sauran shugabannin jam’iyyar na ƙasa.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban APC na Jihar Filato, Rufus Bature, ya bayyana ƙaddamar da kwamitin a matsayin wani muhimmin mataki na samar da tsari guda na gudanar da kamfen gabanin babban zaɓen 2027

By ukarofi

Leave a Reply