
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu mutane guda biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mummunan kisan wata mata mai shekaru 35, Fatima Abubakar tare da ‘ya’yanta su shida a Unguwar Ɗorayi Chiranchi Quarters da ke Kano, wanda ya auku a ranar 17 ga Junairu, 2026.
Haka kuma, kotun ta yanke wa Umar Auwalu mai shekaru 23 ɗan unguwar Sabuwar Gandu Quarters da Yakubu Ɗayyabu mai shekara 21 na Sabon Gida hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan kitsa makircin aikata kisa da fashi da makami.
Da yake gabatar da hukunci kan shari’ar, Mai Shari’a Saminu ya bayyana al’amarin a matsayin laifi na musamman mai tayar da hankali, inda ya ce waɗanda aka samu da aikatawa ‘yan uwa ne ga mamatan da ya dace a ce sun zama masu ba su kariya.
An shaida wa kotun cewa Fatima ce ta buɗe wa ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara ƙofa a lokacin da ya je gidansu tare da ɗan rakiyarsa ba tare da sanin suna shirin ƙaddamar da farmaki a gidan nata ba. Mai Shari’ar ya ce waɗanda aka yi ƙarar sun yi amfani da yardar da marigayiyar take da shi akansu ne wajen aiwatar da mummunan manufar tasu da ta yi ajalinsu su bakwai.
Alƙalin ya bayyana cewa, rasuwar Fatima ya wuce rashin mutum guda duba da halin kasancewarta uwa da ake fatan ta zama ginshiƙin cimma kyawawan manufofin ‘ya’yanta a rayuwa. Ya kuma jajenta wa iyalan marigayan musamman Haruna Bashir, wato mijin matar kuma uban ‘ya’ya shidan, wanda aka bari cikin halin ƙunci da jimamin al’amarin.
Yayin ayyana hukuncin, alƙalin ya kafa hujja da aya ta 45 a sura ta biyar (Ma’ida) cikin Al-Ƙurani Mai Girma da ke magana kan wanda ya kashe a kashe shi, kana ya yanke hukuncin kisa ga mutum biyun. An same su ne da hannu a kisa ba bisa haƙƙi ba, laifin da ya ci karo da Sashe na 221 na dokar Manyan Laifuka ta Penal Code kan kisan Fatima da ‘ya’yan nata shida. Haka kuma, an umarci da su yi zaman kurkuku tare da aiki mai wahala bisa samun su da laifin makirci da fashi da makami.
Mutum na huɗu da ake ƙara a shari’ar, Isyaku Yakubu ɗan shekara 40, an wanke shi daga tuhume-tuhumen da aka masa kuma an sallame shi. Yayin da Auwalu ya amince da laifinsa da kuma neman sassauci, sai Ɗayyabu kuma wanda ya yi ƙoƙarin wanke kansa kuma ya shiga sahun masu musanta abin da ake zarginsu a kai.
