Ƙungiyar malaman kwalejin ilimi ta buƙaci Gwamna Radda ya aiwatar da alawus ɗin ₦70,000 na sufuri

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar malaman kwalejojin ilmi ta ƙasa, COEASU, ta buƙaci Gwamnatin jihar Katsina da ta aiwatar da matsayar da a ka cimmawa tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, dangane da walwala da jin daɗin malamai da ke a kwalejojin Ilmi biyu da ke a cikin jihar.

Buƙatar hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da a ka aikewa Gwamna Dikko Umar Raɗɗa, ɗauke da rattaɓa hannun sakatare janar na ƙungiyar malaman, Dakta Churchill Chukwunonso.

Ƙungiyar ta bayyana cewa sun gabatar da buƙatar hakan ne a madadin shugabancin ƙungiyar na ƙasa da mambobin ta, biyo bayan taron sulhu da ya wakana tsakanin ƙungiyar ƙwadago da gwamnatin tarayya a ranar 27 ga watan Oktoba na shekara ta 2026.

Manyan makarantun da waɗannan buƙatu su ka shafa a jihar Katsina su ne kwalejin ilmi ta Isah Kaita da ke Dutsinma, da kuma kwalejin ilmi da ayyukan dhari’a ta Yusuf Bala Usman da ke Daura.

COEASU dai na buƙatar gwamnatin jihar Katsina ta aiwatar da yarjeniyoyin da a ka cimma domin kyautata walwala da jin daɗin mambobin su.

Wani muhimmin ɓangare da ke cikin wasikar shi ne buƙatar aiwatar da tallafin sufuri na naira dubu 70 na wata-wata domin ‘ya’yan ƙungiyar, wanda a ke sa ran farawa daga watan Nuwamba har tsawon watanni shida da ke tafe. Kamar yadda COEASU ta bayyana, manufar wannan tallafi ita ce sauƙaƙa wahalhalun sufuri da kuma ƙara ƙarfafa malaman don su gudanar da ayyukan su yadda ya cancanta.

Haka zalika ƙungiyar ta yi kiran a duba gami da gyara haƙkoƙin da su ka shafi albashi da biyan bashin alawus na nalaman kwalejojin Ilmi. Ta ce yarjejeniyar ta ƙunshi amincewar gwamnatin tarayya a kan wasu kuɗaɗen alawus na musamman (peculiar allowance), da ya soma aiki daga ranar ɗaya ga watan Mayu, haɗe da biyan bashi (arrears) da za a fara biya a watan Nuwamba, a bisa kaso uku (3 instalments).

Daga nan sai ƙungiyar ta COEASU ta buƙaci Gwamnatin jihar Katsina da ta haɗa ma su ruwa da tsaki daga ɓangarorin ƙudi da ilmi da hukumomin gudanarwar kwalejojin Ilmi da wakilan ƙungiyar, domin samar da hanyoyin warware waɗannan buƙatu.

Idan dai za a iya tunawa, a cikin watan Satumba na shekara ta 2026, ƙungiyar ta gabatar da wata takarda ga Gwamna Dikko Raɗɗa, a kan buƙatar aiwatar da kaso 40 cikin ɗari na wani alawus na musamman (CATA) a waɗannan kwalejojin Ilmi biyu. Sai dai ƙungiyar ta damu ƙwarai cewar har yanzu ba su ji komai ba daga gwamnatin tun gabatar da buƙatun.

Waɗannan batutuwan sun cigaba da kasancewa abubuwa ma su matuƙar muhimmanci da ƙungiyar ta COEASU ta sanya a gaba a dukkanin taruka da zaman da ta ke gudanarwa.

COEASU ta bayyana gamsuwa da himmatuwar Gwamna Raɗɗa wajen bunƙasa harkokin Ilmi da inganta jin daɗin malamai, a yayin da kuma ta ke kiran a hanzarta dubawa da kuma aiwatar da waɗannan buƙatu da su ka gabatar.

By ukarofi

Leave a Reply