Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Olujuwon Obasanjo, ɗan tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya shiga ƙungiyar fafutukar neman sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta PBAT Door-to-Door Moɓement, inda aka naɗa shi mai ba ƙungiyar shawara ta musamman kan harkokin siyasa.
Olujuwon ya bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin ganin Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027, yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja ranar Laraba.
A yayin ziyarar, Mai Gudanar da Ayyukan ƙasa na ƙungiyar, Sunday Adekanbi Asuku, ne ya tarbe shi tare da zagaya da shi sassan hedikwatar domin ya fahimci ayyukan da ƙungiyar ke gudanarwa. Olujuwon ya bayyana naɗin da aka yi masa a matsayin babban matsayi da alfahari, inda ya yaba wa ƙungiyar bisa yadda take kai saƙon manufofin gwamnati ga al’umma, taimaka wa jama’a da kuma wayar da kai kan ayyukan gwamnatin Tinubu.
Ya ce ya daɗe yana bibiyar ayyukan ƙungiyar, kuma yana matuƙar jin daɗin irin ƙoƙarin da take yi. Ya bayyana aniyarsa ta bayar da gudummawar da ta dace domin cimma manufofin ƙungiyar da kuma tabbatar da sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027. A cewarsa, Shugaba Tinubu ya fara tafiyar mulkinsa da kyakkyawan mataki, saboda haka akwai buƙatar ’yan Nijeriya, musamman matasa, su haɗa kai wajen tallafa wa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa da kuma tabbatar da ɗorewar mulki.
Ya bayyana cewa ƙasar ta samu ci gaba a wasu fannoni, ciki har da biyan albashi, bunƙasa ababen more rayuwa da samar da damarmakin zuba jari, yana mai cewa ya kamata a kiyaye nasarorin da aka samu tare da ƙara inganta su. Olujuwon ya ce yana da yakinin cewa ci gaba da bai wa Shugaba Tinubu goyon baya zai ba gwamnatinsa damar gina kan nasarorin da ta samu tare da samar wa ’yan Nijeriya ƙarin alfanun mulki. Ya kuma bayyana cewa ya kasance mamba a jam’iyyar APC tun daga shekarar 2014, yana mai cewa iyalinsu na bai wa kowane ɗa damar kasancewa da ra’ayinsa na siyasa ba tare da ƙiyayya ko gaba ba.
Da yake nasa jawabin, Mai Gudanar da Ayyukan ƙasa na ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement, Kwamared Sunday Adekanbi Asuku, ya yi maraba da shigowar Olujuwon, inda ya bayyana shi a matsayin gogaggen ɗan siyasa mai ƙwarewa a harkokin jagoranci da tafiyar da mulki. Adekanbi ya ce yana da yaƙinin cewa ƙwarewar Olujuwon da fahimtarsa kan dabarun tattara magoya baya za su ƙara wa ƙungiyar ƙarfi tare da taimaka mata wajen faɗaɗa ayyukanta a sassan ƙasar.
