Daga GAMBO ISA a Abuja
Mai Martaba Sarkin Gamawa, Alhaji Adamu Abdulkadir Adamu, ya yaba wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, bisa ayyukan ci gaban da yake gudanarwa a jihar, tare da ƙirƙiro sababbin masarautu da kuma karrama sarakunan da suka cancanta.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da wakilin jaridar Blueprint Manhaja, inda ya yi bayanin dalilan da suka sa ya karrama Gwamnan da sarautar gargajiya ta Dan Lawan of Gamawa.
Ya ce ya ba Gwamnan wannan sarauta ne bisa jajircewarsa wajen samar da ci gaba ga al’ummar Jihar Bauchi, musamman ƙirƙiro sababbin masarautu da kuma ba sarakunan da suka cancanta damar taka rawar da ta dace wajen tafiyar da al’amuran al’ummominsu.
Mai Martaba Sarkin ya kuma yaba wa sauran sarakunan da aka karrama bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban al’ummominsu.
Ya bayyana cewa ƙasar Gamawa tana da tarihi mai girma, tare da alaƙa da Daular Kanem-Borno da kuma Daular Usmaniyya, yana mai cewa shi ne sarki na farko a Masarautar Gamawa.
Sarkin ya ƙara da cewa Gwamnan Bauchi ya samar da ci gaba mai yawa a fannoni daban-daban domin inganta rayuwar al’ummar jihar, musamman mutanen ƙasar Gamawa.
Ya kuma bayyana cewa Gwamnan ya bayar da umarnin gina babbar kasuwar zamani a Gamawa domin inganta harkokin kasuwanci da bunƙasa tattalin arzikin al’ummar yankin.
Haka kuma, Mai Martaba Sarkin ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da addu’ar samun zaman lafiya, tare da kasancewa masu kyawawan ɗabi’u da tarbiyya a kowane lokaci.
Ya kuma yi kira ga hakimai da dagatai da su ci gaba da kiyaye mutuncin jama’a, tare da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, tausayi da adalci.
A ƙarshe, Sarkin ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban Jihar Bauchi, yana mai cewa al’ummar Gamawa ba su da abin da za su ce masa illa godiya da yi masa fatan alheri.
