
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta ce, ta kama wani ɗan daba mai suna Umar Usman da aka fi sani da Ta’ambo ka zargin sa da hannu a ayyukan dabanci, ƙwacen waya da hare-hare akan jami’an tsaro a unguwar Rimin Kebe da kewayenta da ke jihar.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya faɗi haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, 6 ga Nuwamba, 2026 inda ce matashin mai shekaru 25 yana cikin jaddawalin waɗanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zargin sa da hannu a miyagun ayyukan a yankin.
Wasu jami’an sirri da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Zango Police Division ne suka kama wanda ake zargin da misalin ƙarfe 8:40 na daren wayewar ranar Juma’a, bayan tsawon makonni ana tattara bayanan sirri kan yadda za a kama shi, kamar yadda kakakin ya bayyana.
A cewar sanarwar, ana zargin Usman, wanda ɗan Rimin Kebe ne da shirya ayyukan dabanci, ciki har da raunata wani jami’in tsaro da ƙwacen waya da wasu ababe masu daraja a yankunan Rimin Kebe, Ramin Research Area da kuma Asibitin Galula. Rundunar ta ce, an yi nasarar cafke shi ne bayan ƙorafe-ƙorafen al’umma akansa da rahotannin sirri da suka alaƙanta shi da laifukan da kuma labari daga ɓangaren ‘yan yankin kan zirga-zirgarsa.
Akan haka ne mazauna da jagororin al’ummar yankunan suka bayyana kamen a matsayin babbar nasara, wadda ta sanya suke fatan hakan ya zama silar kawo ƙarshen ayyukan dabanci a unguwannin nasu. CSP Kiyawa ya bayyana cewa a yanzu haka ana gudanar da bincike akansa, inda ake ƙoƙarin kama sauran ‘yan dabarsa da ƙwato kayayyakin da aka sace da makamai kana a miƙa shi ga kotu domin ta yi hukunci.
Kwamishinan ‘yan sandan, Ibrahim Bakori, ya yaba wa jami’an ofishin Zangon bisa ƙwarewarsu sannan ya kirayi al’umma da su cigaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen daƙile aikata miyagun laifuka a unguwanninsu.
