2027: NDC ta yi zargin hana wuraren taruka da otel ga ‘yan adawa a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta Nigeria Democratic Congress (NDC) ta zargi jam’iyya mai mulki All Progressives Congress (APC) da sanya wa otel-otel takunkumi a Birnin Tarayya Abuja domin hana ‘yan adawa damar samun wuraren da za su riƙa gudanar da taruka da wasu harkokinsu.

Rahotanni sun ce, wannan zargi na ƙunshe ne a wata takarda da Sakataren Yaɗa Labaran NDC na Ƙasa, Osa Director ya fitar a ranar Alhamis, inda ya yi iƙirarin cewa yunƙurin taƙaice damarmakin da tsarin dimukraɗiyya ya bai wa ‘yan adawa na cigaba da fuskantar matsi. Ya yi zargin cewa otel ɗin Rockview ya soke buƙatar gudanar da tarukan NDC biyu bayan da fari ya amince ya bai wa jam’iyyar gurin taro.

A cewarsa, lokacin farko da hakan ya faru shi ne na ranar 2 ga Yuni, 2026, a sa’ilin da otel ɗin ya soke buƙatar taron kwamitin zartarwar NDC ana gab da aiwatarwa, yana mai cewa APC na amfani da ikonta wajen nuna wariya ga ‘yan adawa kan samun wuraren taruka a otel-otel da makamantansu a Abuja. “Haka ma BON Hotel da ke Wuse, Abuja, sun ƙi mu yi amfani da wurinsu domin gudanar da zama duk da cewa mun cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata,” inji shi.

Sakataren ya ƙara da cewa, ƙiris ya rage a lalata taronsu na ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe bayan otel ɗin da suka biya kuɗi domin gudanar da taro ya buƙaci ya mayar wa jam’iyyar kuɗinta, inda ya ce mata ba zai iya samar da wajen taron nasu ba. Ya ce, daga bisani otel ɗin ya bar NDC ta yi taron bayan nuna turjiya kan lallai sai an ba ta damar aiwatar da shi saboda ta riga ta biya kuɗi.

Kazalika, ya ce ‘yan Nijeriya sun cancanci samun walwala sama da ta yanzu, don haka jam’iyyar a shirye take ta yi wa ƙasar hidima bisa jajircewa da kishi muddin aka zaɓe ta a babban zaɓen 2027.

By Babaji

Leave a Reply