Hukumar Shari’a ta dakatar da alƙalai uku, ta ja kunnen takwas kan rashin ɗa’ar aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) ta sanar da dakatar da wasu alƙalai guda uku na tsawon shekara guda ba tare da biyan su albashi ba da kuma gargaɗin wasu guda takwas bisa ayyukan rashin ɗa’ar aiki, ciki har da tsare wasu da shari’a ta haɗa da su ba bisa doka ba, saɓa wa ikon shari’a da kuma bijire wa aiki da tsare-tsaren shari’a.

Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) Mai Shari’a Kudirat Kekere Ekun, ta kuma amince da wasu wasiƙun jan kunne akan wasu jojji uku bayan gudanar da wani bincike kan ƙorafin yadda suke gudanar da shari’o’in kotu. An ɗauki waɗannan matakai ne a ranar 3 ga Nuwamba, 2026 yayin zaman majalisar karo na 112.

Alƙalai ukun da aka dakatar sune Mai Shari’a Hannatu Mohammed Kabir ta Babbar Kotun Jihar Nasarawa, Babban Alƙali Mohammed Sani Salihu na Kotun Ɗaukaka Ƙarar Shari’ar Jihar Jigawa da kuma Mai Shari’a Sobere Biambo na Babbar Kotun Jihar Ribas.

An dakatar da Alƙali Hannatu ne bisa bayar da izinin kamawa da tsare wani mutum na tsawon kwana 58 kan zarginsa da rashin biyayya ga umarnin kotu ba tare da amfani da hukunce-hukuncen doka ba. Sannan majalisar ta dakatar da ita daga samun ƙarin matsayi na tsawon shekara uku, saboda rashin bai wa wanda aka tsaren damar sauraron sa.

Shi kuwa Grand Ƙadi Salihu na Jigawa, an dakatar da shi ne kan samun sa da hannu a sake buɗe wata shari’a da kotun FCT Upper Area Court ta Abuja ta yi hukunci a kai. Bincike ya nuna cewa ya wuce ƙarfin ikonsa ta hanyar kafa kwamitin domin yin nazari kan hukuncin, da kuma miƙa wa wani alƙali akalar shari’ar, wanda ya samu sabuwar hujja tare da yin sabon hukunci a kai. Alƙali Biambo na Ribas kuwa, an yanke masa hukuncin ne kan bayar da umarnin kama wasu mutane da tilasta wa kowannensu biyan tarar N300,000 kan rikicin fararen hula ba tare da kiyaye ƙa’idojin doka ba. Sannan, an dakatar da Alƙali Salihu da Mai Shari’a Biambo su ma daga ƙarin matsayi na tsawon shekara uku.

Haka kuma, majalisar ta ja kunnen Mai Shari’a Kayode Agunloye na Babbar Kotun Abuja bisa gudanar da wasu al’amuran bayan shari’a da suka ƙunshi ƙwace kadarori da suka haɗa da bankin First Bank, duk da cewa an janye ƙarar kuma an kore ta.

Sannan NJC ta amince da gargaɗin wasu alƙalai, ciki har Mai Shari’a Bello Kawu, wanda ya bayar da belin wucin-gadi ga tsohon Antoni Janar na Ƙasa (AGF), Abubakar Malami, duk da cewa akwai umarnin kotu daga wani alƙali na a cigaba da tsare shi. Kazalika, an gargaɗi Alƙali Danjuma Oyigbenu da Isa Ebini kan yin hukuncin ɗaukaka ƙara a wajen wa’adin kwanaki 90 da doka ta bayar da dama.

Sauran waɗanda majalisar ta yi wa gargaɗi ko taka sanya ido kanssu sun haɗa da Alƙali Mohammed Zubairu na Babbar Kotun Abuja; Alƙali C. A. Ogbuagor na Babbar Kotun Enugu; da kuma Alƙali Chibuike Azuama na Babbar Kotun Jihar Imo.

A wani labarin kuwa, majalisar ta amince da naɗin wasu masana shari’a 28 a matsayin alƙalan kotuna daban-daban na jihohin Kano, Ebonyi, Edo, Adamawa, Ogun, Filato da kuma Adamawa .

By Babaji

Leave a Reply