Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi.
Hukumar bincike da magance cutar sankara ta ƙasa, (National Institute for Cancer Research and Treatment, NICRAT), ta fara tantance mata 200 a jihar Kebbi domin gano masu ɗauke da cutar sankara ta mahaifa (Cervical Cancer), a ƙarƙashin shirinta na share-fage wanda ke gudana a jihohi shida na ƙasar nan daga kowane ɓangaren yankin siyasa na Najeriya ( geo-political zones).
Aikin tantancewar yana cikin ƙwazon da akeyi na bai ɗaya wurin hana yaɗuwar cutar sankara da kuma aiwatar da shirin tsare-tsaren iyali na tazarar haihuwa na ƙasa.
Wannan aiki na gudanane a asibitin yanki matakin farko na shan magani da ke Unguwar Takalau, Birnin Kebbi, ƙarƙashin kulawar likitan da ke bai wa hukumar NICRAT shawara akan takamaimen shirin hana yaɗuwar cutar sankara, Dakta Ishaq Lawal.
Dakta Ishaq Lawal wanda ƙwararren likitan mata ne masu ɗauke da juna-biyu (Gynecologist) da ke aiki a asibitin koyarwa na Gwamnatin Tarayya, Birnin Kebbi, ya ce tantancewar da ake yi, ana bin sahihiyar hanyar yin gwaji wadda hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta amince da ita, sannan kuma game da wani tsarin da ake kira NICE-SCAN.
Ya yi bayanin cewar shi wannan tsarin ya ƙunshi a gano cutar sankara tun tana jaririya, sannan kuma a magance ta nan-take, domin ceton rayukan al’umma.
Likitan ya ce za’a inganta duk asibitin da ake tantance mata, sannan kuma a horas da masu aikin kiwon lafiya.
Dakta Ishaq Lawal ya ce hukumar NICRAT ta samar da duk kayayyakin gwaji da tantance masu ɗauke da cutar ta sankara, sannan kuma hukumar za ta kawo kayayyakin maganin cutar domin amfanin waɗanda ke ɗauke da ita.
Ya sanar da cewar NICRAT ta na son ta ga cewar babu wata mace da ke mutuwa sanadiyyar cutar sankara ta nono ko sankara ta mahaifa, domin ana iya kare afkuwar haka.
Dakta Ishaq Lawal ya yi sharhin cewar kamuwa da cutar sankara ba ciwon ajali ba ne, idan an gano da wuri-wuri, amma akwai hatsari da illa mai girma idan ta rigaya ta yi tsanani ga jikin mai ɗauke da ita, ko kuma ba’a magance ta ba cikin lokaci.
Dalilin haka, ya ce hukumar tana shirin kai kayayyakin magani na zamani na sankara zuwa asibitocin yankuna, da manyan asibiti da kuma asibitocin koyarwa, sannan kuma a ƙara horas da likitocin da za su kula da masu ɗauke da cutar.
Dakta Ishaq Lawal ya ce ma’aikatan lafiya da suka samu horaswa a ƙarƙashin shirin da ake gudanarwa a yanzu, sune masu aikin jinya (Nurses) da masana kimiyyar binciken cutattuka (Laboratory Scientists) da kuma masu adana bayanai na majinyata (record unit).
Ya ce abinda ake da buƙata shine duk masu ɗauke da cutar sankara, an yi masu magani sun warke.
A sharhin da tayi, Hajiya Zainab Ahmed, wadda ta wakilci darakta-janar na hukumar NICRAT, Farfesa Usman Aliyu, ta ce shirin na tantance masu ɗauke da sankaran mahaifa, gwamashi za’ayi wurin aiwatar da shirin tsare-tsaren iyali na ƙasa.
Ta ce abinda ake so, shine a duk lokacin da wata mace ta je asibiti da nufin amfana da tsare-tsaren iyali dangane da haihuwa, sauki ne gareta a tantance ta wurin sanin halin da ta ke ciki, ko tana ɗauke da cutar sankara ta mahaifa ko a’a.
Zainab ta yi bayanin cewar hukumar NICRAT ta lashi takobin sauƙaƙa ma mata wahalhalun da ke tattare da cutar sankara ta mahaifa.
Ta ce wasu mata mazauna yankunan karkara, sun ɗauki cewar duk macen da ta kamu da cutar sankara, abin kunya ne, saboda haka sai su ɓoye bayanin haka, ba su fitowa fili su ce suna ɗauke da ita, kuma rashin magana babban hatsari ne.
Zainab ta ƙara da cewar hukumar NICRAT ta tashi tsaye wurin gangami da ilmantar da mata akan muhimmancin su fito ayi masu gwaji ko suna ɗauke da cutar domin a magance ta.
