
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar adawa ADC, ta sanar da wajen da za ta gudanar da gangamin buɗe yaƙin zaɓen ɗan takararta na shugaban ƙasa yayin shirye-shiryen zaɓukan 2027.
Kodinetan kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC na Sakkwato, Sanata Ibrahim Lamiɗo ne ya sanar da haka, inda ya ce za a fara taron a Sakatariyar ADC da ke kan hanyar zuwa Ilorin a Jihar Sakkwato, ranar Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.
A cewarsa, muhimman masu ruwa da tsaki da sauran mambobin jam’iyyar sun riga sun fara shirin halartar babban taron.
Bayan da aka samu zarge-zargen wulaƙanci da danniya akan jam’iyyar da mambobinta a jihar, ADC ta ɗauki matakin ɓoye gurin taron da fari bisa abin da ta kira da dalilan tsaro, wadda a yanzu kuma ta bayyana wa al’umma.
A ranar Juma’a ne dai wasu ‘yan bindiga suka buɗe wa ayarin motocin ɗan takarar gwamnan ADC na Sakkwato, Manir Muhammad Ɗan’iya wuta, a kusa da filin jiragen sama na Sultan Abubakar na III, inda ya samu nasarar tsira ba tare da wani rauni ba.
