Babaji

5432 Posts

2027: Ba kowane taron yaƙin neman zaɓe zan halarta ba saboda harkokin gwamnati, inji Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, akwai yiwuwar ya haƙura da zuwa wasu tarukan yaƙin neman zaɓe a wasu jihohi yayin da yake neman al'ummar Nijeriya su sake zaɓar sa a karo na biyu a zaɓen 2027, saboda akwai buƙatar ya kula da al'amuran shugabanci. Shugaban ya yi wannan isharar ne yayin da yake magana a taron ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa na Jam'iyyar APC a ɗakin taro na Banquet Hall da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, ranar Laraba. Tinubu ya ce, an shawarce shi da kada ya bari yaƙin neman…
Read More

El-Rufa’i: Shaida ya yi zargin ware Dala 600,000 don dakatar da binciken EFCC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani shaida a shari'ar rashawa ta tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya yi zargin cewa an ware Dala 500,000 da wani Dala 100,000 domin bai wa jami'an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) a matsayin cin hanci saboda su dakatar da bincike akan wasu kamfanoni a shari'ar da ake masa. An gudanar da zaman ne na tsawon sa'o'i tara, wanda Mai Shari'a Darius Khobo na Babbar Kotun Jihar Kaduna ya jagoranta a ranar Talata, kana ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranakun 30 ga Nuwamba da kuma 1 ga Disamba, 2026.…
Read More

INEC ta sanar da sabbin lokutan zaɓukan 2027, ta samar da tsarin lambobin QR don gano wuraren karɓar katin zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a Jihar Legas, ta samar da tsarin lambobi na Quick Response (QR) domin taimaka wa masu zaɓe gano cibiyoyin karɓar katin zaɓensu (PVC) gabanin babban zaɓen 2027, yayin da hukumar ta kuma sanar da sababbin lokutan zaɓe bayan sauya fasalin dokar zaɓe. INEC ta ce, za ta wallafa lambobin na QR a shafukanta na sada zumunta da sahihin shafinta na yanar gizo domin bai wa masu zaɓe damar gano inda za su karɓi katinsu cikin sauƙi yayin da babban 2027 ke cigaba da ƙaratowa. Kwamishinan zaɓen Legas, Farfesa Ayobami…
Read More

‘Yan bindiga sun ƙone gawar jami’in shige da fice bayan halaka shi a Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) reshen Neja, ta tabbatar da mutuwar wani jami'i da 'yan bindiga suka farmaka yayin wani atisaye a Jihar Neja. Kakakin hukumar, DSI Mukhtar Abubakar ne ya tabbatar da faruwar al'amarin a wata sanarwa da ya fitar a Minna, ranar Litinin. Abubakar ya ce, an farmaki Mataimakin Sufuritandan Shige da Ficen mai daraja ta I (ASI I), Ibrahim Babagiwa ne tare da wani sufeto a ƙauyen Woko da ke yankin Tungan Waya, a ranar 6 ga Oktoba, a lokacin da jami'an suke gudanar da sintiri a yankin. A…
Read More

2027: Kotu za ta yanke hukuncin gyaran ƙarar Atiku ta neman soke cancantar Tinubu a 20 ga Nuwamba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai Shari'a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya sanya ranar 20 ga watan Nuwamba, 2026 domin yin hukunci akan ƙorafin da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya shigar, wanda ke neman a yi wa ƙararsa kwaskwarima akan Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC kan zargin shugaban Nijeriyar da amfani da takardar shaidar kammala hidimar ƙasa (NYSC) ta bogi. Mai Shari'ar ya ayyana ranar ne bayan lauyan Atiku, Joseph Silas da lauyoyin ɓangaren waɗanda ake ƙara suka gabatar da ba'asinsu da tafka muhawara akan…
Read More

An halaka mutum 20 yayin da ‘yan bindiga suka yi wa ‘yan kasuwa da jami’an tsaro kwanton-ɓauna a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu 'yan bindiga sun halaka aƙalla mutane 20, ciki har da sojoji da 'yan sanda bayan sun yi wa wata tawagar ƙananan 'yan kasuwa da ke tafiya tare da rakiyar sojoji kwanton-ɓauna a Zamfara. Al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar, a lokacin da 'yan kasuwar suke kan hanyar tafiya daga yankin Gwashi zuwa kasuwar Nasarawa da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a cewar Reuters. Wani ɗan yankin mai suna Musa Ɗanladi, wanda ya ce ya taimaka wajen ɗauko gawarwakin, ya shaida wa Reuters cewa, sojoji huɗu, 'yan sanda uku da…
Read More

Tsofaffin sojoji sun tare mashigar hukumar fansho a Abuja kan rashin biyan haƙƙoƙinsu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata tsofaffin jami'an sojoji suka yi dandazo a mashigar Hukumar Fanshon Sojoji da ke yankin Kubwa a Abuja, inda suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa ga gyare-gyaren da aka yi wa tsarin fanshonsu tare da zargin rashin biyayya ga biyan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi. An ga yadda tsofaffin sojojin suka tare mashigar ofishin da tantina da kujeru tun da misalin ƙarfe 8 na safe, suna nuna rashin gamsuwa da aiwatar da gyare-gyaren, yayin da sojoji suka hana su shiga cikin farfajiyar ofishin. Wannan na zuwa ne makonni…
Read More

Tinubu ya ba wa Wike da Adeleke muƙami a kwamitin yaƙin neman zaɓensa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC ta naɗa Ministan Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke a matsayin kodinetoci a kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. Wike zai riƙe muƙamin kodineta a Jihar Ribas da Abuja, yayin Adeleke a ɗaya gefen, an naɗa shi a matsayin kodineta a Jihar Osun, a cewar sabon jaddawalin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar. Waɗannan naɗe-naɗe na zuwa ne gabanin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen, wanda aka tsara yi a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026 a babban ɗakin taro na Banquet Hall…
Read More

Amurka ta yi barazanar janye tallafin soji ga Nijeriya kan ɗaukar ƙananan yara aikin soja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Amurka ta sanya Nijeriya a jerin ƙasashen da suka saɓa wa Dokarta ta Haramta Ɗaukar Ƙananan Yara Aikin Soja (CSPA), tana mai gargaɗin hakan ka iya janyo ta sanya wa Nijeriya takunkumin horar da sojoji, siyar da makamai, ɗaukar nauyin sojojin waje da haɗin kai kan tsaro daga ranar 1 ga Oktoba, har sai an samu alfarmar Shugaba Donald Trump. Wannan al'amari ya biyo bayan rahoton 2026 da Ma'aikatar Kula da Lamuran Safarar Ɗan-adam ta Amurka ta fitar, wanda ya zayyano ayyukan cigaba da ɗauka da amfani da ƙananan yara daga ƙungiyoyin Boko Haram…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta shigar da sabuwar ƙara akan Adeyemin hukumar bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ra shigar da sabuwar ƙara akan Adeniyi Adeyemi, Darakta-Janar na hukumar da aka yi zargin ta bogi ce, wato Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC). Lauya ga Antoni Janar na Ƙasa, Rotimi Oyedepo (SAN) ya shaida wa Mai Shari'a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya cewa sun riga sun shigar da sabuwar ƙara a Babbar Kotun Abuja. Akan haka ne ya nemi alƙalin ya yi watsi da ƙarar a babbar kotun tarayyar. Ganin cewa lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu (SAN) bai yi inkarin buƙatar ba, Alƙali Umar ya yi watsi…
Read More