
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke yankin Apo a Abuja, ta umarci da a karɓe kadarorin da aka danganta su da ‘yar kasuwa, Aisha Achimugu tare da damƙa su ga Gwamnatin Tarayya.
Rahotanni sun bayyana cewa, ababen da kotun ta umarci a ƙwace sun haɗa da saraƙuna masu darajar Naira biliyan 4.645, motocin alfarma guda 11 masu darajar biliyan N4.293, Dala 50,000 na tsabar kuɗi da kuma ƙarin wasu miliyan N30.
Mai Shari’a Jude Onwugbuzie ne ya bayar da umarnin a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2026 yayin gabatar da hukunci akan ƙara da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar na neman ƙwace kadarorin attajirar.
A yayin hukuncin, kotun ta bayar da umarnin karɓe kadarorin na dindindin da miƙa su ga gwamnatin tarayyar bayan ƙorafin EFCC’n.
Wannan umarni shi ne na matakin ƙarshe da EFCC ta gabatar akan kadarorin da aka alaƙanta su da Achimugu.
