Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ƙasar Saudiyya ta ayyana jihar Kebbi a matsayin jihar da ta fi kowace jiha daga jihohin Nijeriya a kan aikin hajjin bana.
Ƙasar Saudiyyar ta bayyana cewa wannan karramawar ta biyo bayan nazarin da ta yi ne bisa ga la’akari da yadda jami’an hukumar aikin hajjin Kebbi ke bai wa alhazzan ta cikakkiyar kulawa ƙarƙashin jagorancin Alhaji Faruku Aliyu (Enabo) da goyon bayan gwamnatin jihar.
Da ya ke zantawa da waƙilin jaridar Blueprint Manhaja Alhaji Faruku Enabo ya bayyana cewa wannan ya samu asali ne kan irin sadaukarwar Gwamna Nasir Idris na bada dukkanin abinda hukumar jin daɗin alhazzai ta Jihar Kebbi ke buƙata.
Ya ƙara da cewa ba shakka wannan ita ce shekarar da ba zai taɓa mantawa da ita a rayuwar sa bisa ga irin nasarar da ya samu ba saboda cikin ikon Allah tun daga farkon aikin hajjin bana har aka kammala ba a sami ko mutum ɗaya da ya rasu ba kuma ba wanda aka kama da wani laifi har zuwa lokacin kammala jigilar alhazzai.
