Ranar abinci ta duniya: Uwargidan Gwamnan Zamfara ta yaba wa manoma mata

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa manoma mata a jihar kan muhimmiyar rawar da suke takawa wajen tabbatar da samar da abinci da kuma bunƙasa harkar noma.

Uwargidan Gwamnan ta yi wannan yabo ne a yau a wurin bikin ranar abinci ta duniya da ƙungiyar mata manoma ta ƙasa (NAWIA), reshen Jihar Zamfara ta shirya, wanda aka gudanar a harabar baje kolin kasuwanci da ke Gusau.

A cikin jawabinta, Hajiya Huriyya Lawal ta ce bikin ya ba da dama ta musamman don yin tunani kan muhimmiyar rawar da noma ke takawa wajen tabbatar da wadatar abinci, da inganta ci gaba mai ɗorewa da kuma inganta rayuwar al’umma.

Ta bayyana kyawawan kayan amfanin gona da aka nuna da kuma yadda mata suka halarci taron da yawa a matsayin shaida ƙarara ta haɗin kai da jajircewa wajen bunƙasa noma, ƙarfafa tattalin arziki da cimma burin samar da isasshen abinci a Jihar Zamfara.

Uwargidan Gwamnan ta musamman yaba wa shugabar ƙungiyar ta NAWIA ta Jihar Zamfara, Hajiya Shemau Nalado, kan shugabanci na ƙwarai, sadaukar da kai da jajircewar da take yi wajen ƙarfafa mata da kuma ciyar da harkar noma gaba a faɗin jihar.

Ta kuma yaba wa mijinta kuma Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, kan jajircewa da goyon baya da gwamnatinsa ke baiwa manoma ta hanyar bada tallafin noma, rabon taki akan kari da sauran tsare-tsare da nufin ƙara yawan amfanin gona da inganta noma.

“Noma shine alfaharinmu kuma shine gadonmu a Jihar Zamfara. Don haka, mu ci gaba da tallafa wa manomanmu, mu ƙarfafa matanmu kuma mu haɗa kai wajen samar da jihar da ke da isasshen abinci kuma mai albarka ga kowa,” in ji ta.

Tun da farko a cikin jawabin maraba da ta gabatar, Shugabar NAWIA ta Jihar Zamfara, Hajiya Shemau Muhammad Nalado, ta ce taken duniya na bana, “Hannu da hannu don kyakkyawan abinci da makoma mai kyau,” yana da matuƙar muhimmanci ga manoman mata saboda yana tunatar da duniya cewa babu tabbacin abinci ba tare da mata ba.

Ta ce a Zamfara, mata su ne ginshiƙin noma, domin su ne ke shuka, suke gyaran gona, suke girbi kuma suke ciyar da iyalansu da ƙasa baki ɗaya, duk da ƙalubalen rashin tsaro da ƙarancin kuɗi.

Hajiya Shemau ta bayyana cewa a halin yanzu ƙungiyar NAWIA Zamfara tana da mata sama da 3,000 a fadin jihar da ke noman shinkafa, gero, gyada, kiwon kaji da noman kayan lambu, inda ta ƙara da cewa kwanan nan hukumar kula da Ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE) ta ziyarci ƙungiyar don tantancewar horon sana’o’in TVET don horar da mata da matasa.

Sai dai, ta lissafa manyan ƙalubalen da manoman mata ke fuskanta a jihar da suka haɗa da ƙarancin samun rance mai sauƙi da tallafi, ƙarancin kayan aikin noma na zamani da injuna, ƙarancin wuraren ajiya da sarrafa amfanin gona, da kuma tasirin sauyin yanayi ga amfanin gona.

Shugabar NAWIA din ta yi kira mai cike da roko ga Gwamnatocin Tarayya da Jiha, Bankin Noma (BOA), abokan ci gaba da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka wa manoman mata a Zamfara da rance, kayan noma da horo.

“In ka karfafa mace manomiya guda, ka ciyar da al’umma gaba ɗaya,” in ji ta.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, wakilan bankin noma, manoman mata daga ƙananan hukumomi 14 na jihar, da kuma ‘yan jarida.

By ukarofi

Leave a Reply