
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Hafsan Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NA), Laftanal Janar Waidi Shaibu ya isa birnin Maidugurin Jihar Borno a ranar Asabar, biyo bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na a gaggauta ceto dukkan mutanen da ke tsere da aka yi garkuwa da su a faɗin Nijeriya.
Shugaban sojojin ya isa birnin ne da misalin ƙarfe 11 na safe bisa umarnin da Shugaban ƙasar ya bayar ga hukumomin tsaro da su yi hoɓɓasa wajen ganin sun ceto waɗanda aka sace da shafe sansanonin ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a sassan ƙasar.
A ranar 15 ga Oktoba ne Ministan Tsaro, Christopher Musa ya ce Shugaba Tinubu ya bada umarnin ga hukumomin tsaro a yayin wani zama da ya ƙunshi jagororin hukumomin wanda ya gudana a ƙarƙashin jagorancin Shugaban a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Tinubu ya kuma bada umarnin cewa kada a bar wani sansani na ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga a ko’ina a Nijeriya ya cigaba da wanzuwa.
Haka kuma, ministan tsaron ya ce Shugaba Tinubu ya faɗa wa jagororin hukumomin tsaro cewa su tabbatar an samu cikakken tsaro ga ‘yan Nijeriya domin su samu damar shiga sahun masu zaɓen da aka shirya yi a Junairu.
