Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Tsohon ɗan takarar neman tikitin takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya fice daga jam’iyyar zuwa APC mai mulki, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Hamma Saleh ya sanar da sauya shekar tasa ne a ranar Juma’a, cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gombe, inda ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su mara wa APC da ’yan takararta baya a dukkan matakan zaɓe.
Ya buƙaci magoya bayansa a faɗin jihar da su haɗa kai da shi wajen goyon bayan jam’iyyar APC, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Sauya shekar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa da fafatawar neman tikitin takarar gwamna ke ci gaba da ɗaukar hankali a Gombe, musamman a cikin jam’iyyar PDP.
Hamma Saleh na daga cikin masu neman tikitin takarar gwamnan jihar a PDP, inda ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fafata da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a neman tikitin jam’iyyar.
Ficewarsa daga PDP zuwa APC na ƙara sauya fasalin siyasar jihar gabanin zaɓen 2027, yayin da manyan ’yan siyasa ke neman ƙarfafa matsayinsu da faɗaɗa tasirinsu a tsakanin masu zaɓe.
Sai dai, a cikin sanarwar da ya fitar, Hamma Saleh bai bayyana takamaiman dalilan da suka sa ya yanke shawarar barin PDP zuwa APC ba.
Ana sa ran matakin nasa zai ƙara zama wani muhimmin batu a siyasar Gombe, yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙoƙarin gina ƙawance da tara goyon baya domin tunkarar zaɓen shekarar 2027.
