
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal ya bayyana cewa marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗauki cewa tsohon mataimakinsa na shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya kara da Bola Tinubu a zaɓen 2023 a matsayin bambaraƙwai.
Babacir Lawal ya ce, da Buhari zai tsinci kansa a halin tsaka-mai-wuya wajen goyon bayan Osinbajo akan Tinubu, wanda tsohon gwamnan na Jihar Legas ne da suke da tsohuwar alaƙa.
A cewarsa, matsayar Buhari ta samu ne bisa tasirin biyayyarsa ga Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin mutumin da ya nemi a zaɓe shi a matsayin shugaba sannan daga baya gaje shi a kujerar. Ya bayyana cewa, Buhari zai ce da Osinbajo zai gwabza da Tinubu a neman kujerar shugaban ko da kuwa yana da cancantar zama a kujerar, da zai samu kansa a halin zullimi da rashin tabbas.
Osinbajo, wanda shi ne Shugaban riƙo a lokacin da Buhari ya tafi ƙasar wajen neman magani, ya ɗauki matakai da dama, ciki har da sallamar Lawal Daura, tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) a Agustan 2018. Wannan mataki ya biyo bayan lokacin da jami’an DSS suka mamaye farfajiyar Majalisar Dokokin Ƙasa a Abuja tare da hana ‘yan majalisar da wasu mutane shiga zauren majalisa.
Tsohon sakataren gwamnatin ya ƙara da cewa, wasu al’amura da suka faru a lokacin sun haɗa da matakin tsohon mataimakin shugaban ƙasar na bai wa wasu mambobin cocinsa muƙaman gwamnati, inda rahotanni suka ce Buhari bai gamsu da matakin nasa ba da wasu ababe da suka faru a lokacin da farfesan yake riƙe da ikon mulkin ƙasar.
