An fara samun sakamako a sauye-sauyen tattalin arziki da muka yi — Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako mai kyau, bayan wani rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa tattalin arzikin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 4.2 cikin 100 a rabin farko na shekarar 2026.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi. Ya ce rahoton ya nuna ci gaba a fannonin bunƙasar tattalin arziki, kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma ajiyar kuɗaɗen waje.

Rahoton Bankin Duniya mai taken Beyond the Federal Purse: How Higher Reɓenues Reshaped State Priorities ya nuna cewa tattalin arzikin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 4.2 cikin 100 a rabin farko na shekarar 2026, idan aka kwatanta da kashi 3.9 cikin 100 a daidai lokacin shekarar 2025.

Bankin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin ƙasar zai bunƙasa da kashi 4.4 cikin 100 a kowace shekara tsakanin 2026 da 2028, yayin da ake sa ran hauhawar farashi za ta ragu zuwa kusan kashi 12 cikin 100 nan da shekarar 2028.

Sanarwar ta ce hauhawar farashi ta ragu daga kashi 27.6 cikin 100 a watan Janairun 2025 zuwa kashi 15.2 cikin 100 a watan Disamban shekarar. Sai dai tashin farashin mai a kasuwannin duniya da matsin lambar farashin abinci sun kawo cikas ga ci gaba da rage hauhawar farashin kayayyaki.

Tinubu ya ce rahoton ya nuna cewa rarar kuɗaɗen da Nijeriya ke samu daga hulɗarta da sauran ƙasashe ta kai dala biliyan 12 a rabin farko na shekarar 2026, kwatankwacin kashi 7.1 cikin 100 na jimillar kuɗaɗen da tattalin arzikin ƙasar ya samar. Adadin ya ƙaru daga dala biliyan 8.6 a daidai wannan lokaci na shekarar 2025.

Haka kuma, ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙasar ta tashi daga dala biliyan 45.5 a ƙarshen shekarar 2025 zuwa dala biliyan 53.8 a ƙarshen watan Agustan 2026, kamar yadda sanarwar shugaban ƙasar ta bayyana.

Rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa kuɗaɗen shiga da ake rabawa tsakanin matakan gwamnati sun ƙaru da kashi 69 cikin 100 a zahiri tsakanin shekarun 2023 da 2025, sakamakon sauye-sauyen da suka haɗa da cire tallafin man fetur da sauya tsarin kasuwar canjin kuɗaɗen waje.

Jihohi ne suka fi amfana da ƙarin kuɗaɗen, inda kuɗaɗen shigarsu gaba ɗaya suka ƙaru da kusan kashi 93 cikin 100 a wannan lokaci, yayin da kashe kuɗaɗensu ya ƙaru da kashi 92 cikin 100.

A cewar rahoton, jihohi sun ƙara kashe kuɗaɗe kan ayyukan raya ƙasa, inda kaso na kuɗaɗen da suke warewa irin waɗannan ayyuka ya tashi daga kashi 46 zuwa kashi 61 na jimillar kashe kuɗaɗensu.

An fi mayar da hankali kan gine-ginen hanyoyi da sauran ababen sufuri, gidaje da noma, yayin da kuɗaɗen da aka ware wa ilimi da lafiya ba su ƙaru daidai da na ayyukan more rayuwar tattalin arziki ba.

Sanarwar Tinubu ta kuma ce jihohi 29 cikin 33 sun ƙara karkatar da kuɗaɗe zuwa ababen more rayuwa, yayin da kuɗaɗen shiga na cikin gida suka ƙaru a zahiri a jihohi 31 cikin 35.

Shugaban ƙasar ya ce sakamakon rahoton ya nuna muhimmancin matakan da gwamnatinsa ta ɗauka, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa kasuwannin canjin kuɗaɗen waje da ƙarfafa tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati.

Sai dai ya amince cewa akwai sauran aiki kafin a tabbatar da cewa ci gaban tattalin arzikin ya inganta rayuwar jama’a, musamman wajen rage farashin abinci da samar da ayyukan yi ga matasa.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da faɗaɗa shirin tallafin kuɗi ga gidaje masu buƙata, bunƙasa noma da inganta damar samun kiwon lafiya mai araha da ingantaccen ilimi.

Bankin Duniya ya jaddada cewa ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziki kaɗai ba zai wadatar ba, sai an inganta yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati da kuma samar da ayyukan more rayuwa domin amfanin jama’a.

By ukarofi

Leave a Reply