Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce shirin sauya tsarin amfani da man fetur zuwa iskar gas mai matsewa (CNG) da motocin lantarki ya jawo zuba jarin masu zaman kansu da ya kai kusan dala biliyan 2.5, yayin da aka ware ko aka yi alƙawarin samar da kusan naira biliyan 250 domin tallafa wa shirin.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manyan editoci da ’yan jarida da aka gudanar ranar Litinin, inda ya yi bayani kan sauye-sauyen tattalin arziƙin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa da tasirinsu ga ƙasar.
A cewarsa, an riga an sauya tsarin amfani da mai na motoci sama da 120,000 zuwa CNG. Haka kuma, an kafa cibiyoyin sauya tsarin motocin sama da 400 da aka amince da su, tare da gidajen mai sama da 90 a faɗin ƙasar.
Ministan ya ƙara da cewa ana ci gaba da aikin kafa wasu gidajen mai 180 domin faɗaɗa damar samun iskar CNG a sassa daban-daban na Nijeriya.
Ya ce shirin na samar da ayyukan yi da damarmakin kasuwanci a yankunan da ake gudanar da ayyukan, yayin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin rage kuɗin sufuri da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Gwamnatin Tinubu ta ƙaddamar da shirin CNG ne bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, matakin da ya haddasa tashin farashin sufuri tare da ƙara matsin tattalin arziƙi ga ’yan Nijeriya.
Daga bisani, gwamnati ta fara inganta amfani da CNG a matsayin madadin man fetur mai rahusa, musamman ga masu motocin kasuwanci.
Sai dai, tsadar sauya tsarin amfani da mai na motoci zuwa CNG na ci gaba da zama babban ƙalubale ga masu ababen hawa.
Kuɗin sauya tsarin motoci na iya kaiwa tsakanin naira 750,000 da naira miliyan 2.5, gwargwadon nau’in mota da injinta. Wannan kuɗin farko na hana wasu masu motoci amfana da shirin, duk da ƙoƙarinsu na rage kuɗin sayen mai.
A watan Satumba, jaridar Nairametrics ta yi nazari kan ƙalubalen da masu motocin da suka koma amfani da CNG ke fuskanta, ciki har da ƙarancin gidajen mai, dogayen layuka da ɓata lokutan aiki.
Ministan ya ce hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ragu daga kusan kashi 27 cikin 100 a watan Janairun 2025 zuwa kusan kashi 15 cikin 100.
Ya kuma ce ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ta Nijeriya ta haura dala biliyan 54 a watan Satumbar 2026, matakin da ya bayyana a matsayin mafi girma cikin kusan shekaru 20.
A cewarsa, ana hasashen tattalin arziƙin ƙasar zai bunƙasa da sama da kashi huɗu cikin 100 a shekarar 2026.
Haka kuma, ya ce rarar asusun hada-hadar kuɗaɗen Nijeriya da ƙasashen waje ta kai dala biliyan 12 a farkon rabin shekarar 2026, idan aka kwatanta da dala biliyan 8.6 a daidai wannan lokaci na shekarar 2025.
Idris ya danganta waɗannan ci gaba da manufofin tattalin arziƙin gwamnatin tarayya, yana mai cewa sauye-sauyen na taimakawa wajen daidaita tattalin arziƙi, dawo da amincewar masu zuba jari da samar da yanayin da zai ba da damar ci gaba mai ɗorewa.
“Alamomin tattalin arziƙin ƙasa sun fara sauyawa zuwa ga alheri, kuma ina kira da a riƙa duba ma’anar waɗannan alkaluma fiye da yadda suke fitowa a kanun labarai,” in ji shi.
Sai dai, ya amince cewa iyalai da dama na ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa, yana mai cewa babban burin gwamnati shi ne tabbatar da cewa ingantattun alkaluman tattalin arziƙi sun haifar da sauƙin rayuwa ga jama’a.
“Alƙawarinmu shi ne tabbatar da cewa ingantattun alamomin tattalin arziƙi sun haifar da ƙarin ayyukan yi, bunƙasar kasuwanci, sauƙin samun muhimman ayyuka da ƙarin ƙarfin sayayya ga iyalan Nijeriya,” inji ministan.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙuduri aniyar ƙarfafa nasarorin da aka samu tare da hanzarta ganin tasirinsu a faɗin ƙasar.
Idris ya ce ayyukan gine-ginen ababen more rayuwa na samar da damarmakin tattalin arziƙi ga ’yan kwangila, masu samar da kayayyaki, injiniyoyi, masu sana’o’i, masu sufuri da sauran ’yan kasuwa.
Ya ce manyan ayyukan raya ƙasa guda huɗu na gwamnatin tarayya sun shafi kusan kilomita 3,000 a faɗin yankunan siyasa shida na Nijeriya, baya ga ɗaruruwan sauran ayyukan hanyoyi, layukan dogo, tashoshin jiragen ruwa, wutar lantarki, lafiya da ilimi.
Ya kuma ambaci wani aikin babbar hanya da aka amince da shi kwanan nan a Jihar Neja, wanda darajarsa ta kai kusan naira tiriliyan 1.5. A cewarsa, aikin zai inganta zirga-zirga a wata muhimmiyar hanya da ake amfani da ita wajen kasuwanci da safarar kayayyakin noma.
Dangane da noma, ministan ya ce gwamnati ta sanya samar da wadataccen abinci a tsakiyar manufofinta na tattalin arziƙi.
Ya ce tallafin injinan noma, samar da kayan aikin noma, ban-ruwa da samun lamunin noma na daga cikin matakan da ake ɗauka domin ƙara yawan amfanin gona a cikin gida, inganta kuɗaɗen shiga na manoma da rage farashin abinci.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wasu cibiyoyin kula da masu fama da cutar kansa guda biyu, wanda ya kai adadin cibiyoyin da aka ƙaddamar zuwa biyar.
Ya ce gwamnati na da burin samar da cibiyoyi 10 a faɗin ƙasar, tare da farfaɗo da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko domin inganta samun kulawar lafiya ga jama’a.
A fannin ilimi, Idris ya ce Asusun Ba da Lamunin Ilimi na ƙasa (NELFUND) ya tallafa wa ɗalibai sama da miliyan 1.6.
Ya ce asusun ya biya kuɗaɗen makaranta sama da naira biliyan 192, sannan ya biya sama da naira biliyan 180 a matsayin kuɗaɗen kula da rayuwar ɗalibai.
A cewarsa, tallafin ya rage wa ɗalibai da iyayensu nauyin biyan kuɗaɗen karatun manyan makarantu.
Ya kuma ce shirin horar da matasa miliyan uku kan fasahohin zamani (Three Million Technical Talent) na faɗaɗa damar matasan Nijeriya na koyon fasahohin kwamfuta, kimiyyar bayanai, tsaron yanar gizo da sauran sabbin fasahohi.
Ministan ya ƙare da cewa zuba jari a matatun mai na cikin gida, ma’adinan da ba na mai ba, masana’antu da kirkire-kirkire na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da samar da ayyukan yi masu ɗorewa.
