BBC ta naɗa Zainab Jumare Mataimakiyar Editan sashen Hausa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gidan rediyo da talabijin na Burtaniya, BBC, ya naɗa Zainab Ibrahim Jumare a matsayin Mataimakiyar Editan Sashen Hausa na BBC.

Naɗin nata ya zo ne makonni kaɗan bayan BBC ta naɗa Haruna Ibrahim Kakangi a matsayin sabon Editan Sashen Hausa na tsawon shekara guda.

Kafin wannan naɗi, Jumare ta yi aiki a matsayin babbar edit a kuma ’yar jarida a Kamfanin Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna (KSMC), inda ta samu ƙwarewa sosai a aikin jarida da samar da shirye-shiryen yaɗa labarai.

Jumare tana da ƙwarewar aikin jarida sama da shekara 12. Ta kuma yi digirin farko da na biyu a fannin Sadarwa da Yaɗa Labarai a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Baya ga aikin editanci da rahoto, tana da ƙwarewa a fannin fassara da gabatar da shirye-shiryen rediyo da talabijin a harsunan Hausa da Ingilishi, waɗanda suka taimaka wajen bunƙasa aikinta a masana’antar yaɗa labarai.

A sabon matsayinta, Jumare za ta kasance mataimakiyar Kakangi, wanda a yanzu yake jagorantar Sashen Hausa na BBC a matsayin editansa.

By ukarofi

Leave a Reply