
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a jihohi guda 12 gabanin zaɓukan 2027. A cewar jaddawalin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar da aka fitar a ranar Alhamis, Tinubu zai buɗe yaƙin neman zaɓen nasa ne a Jihar Kaduna, a ranar 24 ga watan Oktoba kana ya halarci gangami a wasu jihohi 11.
Bayan gangamin na Kaduna, an tsara cewa Shugaban zai je Jihar Ribas a ranar 7 ga Nuwamba, sai Filato a ranar 14 ga Nuwamba da kuma Oyo a 21 ga Nuwamba. Haka kuma, ana sa ran zai halarci taron neman zaɓe a jihohin Borno, Enugu da Bauchi a ranakun 25, 28 da 29 ga Nuwamba.
Sannan, ba a tsara cewa zai halarci tarukan a jihohi 13 ba a Nuwamba. Jihohin sune Kuros-Riba a 2 ga wata, Gombe a ranar 3, Nasarawa 4 ga wata, Ekiti a rana ta 5, Ebonyi a 9 ga wata, Jigawa a 10 ga wata, Ondo a ranar 11, Edo a 12, Yobe a 16, Kebbi 17, Akwa-Ibom 18, Anambara 19 da kuma Benuwai a ranar 30.
Shugaba Tinubu zai cigaba da zuwa gangamin ne a watan Disamba a jihar Sakkwato ranar 5 ga wata, Delta a 12 ga wata da kuma Kano a ranar 17 ga wata. Taruka biyu na ƙarshe da shugaban zai je sune waɗanda za a yi jihohin Adamawa a ranar 4 ga Junairu da kuma Legas a ranar 9 ga Junairu, 2027.
A jimillance, shugaban zai halarci gangamin APC a jihohi 12 daga cikin 36 na Nijeriya da Birnin Tarayya Abuja.
Uku daga cikin jihohin da shugaban ƙasar zai je, wato Oyo, Bauchi da Adamawa, suna da sanannun ‘yan adawa da suke da tasiri ga takarar shugaban ƙasa a zaɓen na 2027. Akwai Seyi Makinde na Jam’iyyar APM, wadda ita ke jagoranci a Jihar Bauchi da kuma Atiku Abubakar na Adamawa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC.
