‘Yan bindiga sun kashe jami’in shige-da-fice tare da ƙona gawarsa a Neja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in Hukumar Shige-da-Fice ta Nijeriya (NIS), tare da ƙona gawarsa bayan sun kai masa hari a jihar Neja.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a jihar, DSI Mukhtar Abubakar, ne ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa da aka fitar a Minna, babban birnin jihar, ranar Litinin.

Ya ce maharan sun kai wa Mataimakin Sufeto na Shige-da-Fice na Mataki na ɗaya, Ibrahim Babagiwa, da wani sufeto hari a ƙauyen Woko, a yankin Tungan Waya, ranar 6 ga Oktoba, lokacin da suke gudanar da aikin sa ido.

A yayin harin, Babagiwa ya rasa ransa, yayin da ɗayan jami’in ya samu raunukan adda, amma ya yi nasarar tserewa.

Sanarwar ta ce jami’in da ya tsira daga harin yana cikin kwanciyar hankali kuma yana samun kulawar likitoci.

Abubakar ya ƙara da cewa an gano gawar Babagiwa a ƙone bayan kwana biyu da faruwar harin, kuma an riga an yi jana’izarsa bisa tsarin addinin Musulunci.

Ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da yaƙi da ƙaura ba bisa ƙa’ida ba da kuma sauran matsalolin tsaro da ke addabar iyakokin ƙasar, duk da ƙalubalen tsaron da ake fuskanta.

Haka kuma, kakakin hukumar ya tabbatar da aniyar jami’an hukumar na ci gaba da sauke nauyin da doka ta ɗora musu.

By ukarofi

Leave a Reply