DOBA ta caccaki gwamnatin Kano kan yanayin makarantu, ta buƙaci ƙarin zuba jari a ilimi

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Makarantar ɗanbatta (ɗanbatta Old Boys Association — DOBA), Alhaji Salisu Lawan Indabawa, ya bayyana damuwarsa kan halin da yawancin makarantun jihar Kano, musamman waɗanda ke yankunan karkara, suke ciki, yana mai cewa rashin kujeru, ƙarancin gyare-gyare da matsalolin masaukin malamai na daga cikin ƙalubalen da ke addabar harkar ilimi a jihar.

Ya ce a wasu makarantu, ɗalibai na zama a ƙasa saboda rashin kujerun zama, yayin da wasu malamai, musamman waɗanda ke koyarwa a makarantun kwana, ke fuskantar matsalar samun masauki. Ya ƙara da cewa akwai malamai da suka yi ritaya amma har yanzu suke zaune a gidajen da aka ba su a makarantu, yayin da wasu ke zama a gidajen da yanayin su ya tsufa kuma bai dace da buƙatunsu ba.

Alhaji Indabawa ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a garin ɗanbatta, bayan kammala taron bayar da tallafin kayan makaranta ga ɗaliban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke ɗanbatta (GSS ɗanbatta).

Tallafin, wanda ya ƙunshi jakunkuna da takalma, gidauniyar NNPC ce ta bayar a ƙarƙashin jagorancin Hajiya Rukayya Abdullahi, tare da haɗin gwiwar Eɓolɓe Charity Trust Foundation, ƙarƙashin jagorancin ɓictoria Edwin. An gudanar da shirin ne a makon da ya gabata.

Shugaban DOBA ya ce ƙungiyarsa ba ta gamsu da yadda ake tafiyar da harkar ilimi a jihar ba, yana mai kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sake duba yadda ake ware kuɗi da gudanar da ayyukan inganta makarantu.

Ya bayyana cewa bai kamata a yi la’akari da adadin kuɗin da aka ware wa ilimi kawai ba, ba tare da duba yadda ake amfani da su wajen inganta yanayin makarantu, samar da kayan aiki da kyautata jin daɗin malamai ba.

Sai dai ya jaddada cewa DOBA ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da wasu muhimman abubuwan more rayuwa a Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke ɗanbatta, domin inganta yanayin karatu da walwalar ɗalibai.

A cewarsa, ƙungiyar ta samar da ruwan sha a makarantar, ta gina ɗakin kwanan ɗalibai mai gadaje 132 tare da kayan aikin da suka dace, sannan ta gina asibitin makaranta mai gadaje shida wanda aka tanada da magunguna da kayan aiki.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta kuma samu gudummawar gina cibiyar kwamfuta, baya ga wasu ayyuka da ta gudanar domin bunƙasa makarantar da inganta yanayin koyarwa da koyo.

Alhaji Indabawa ya ce duk da cewa ƙungiyar na ƙoƙarin rama wani ɓangare na gudummawar da makarantar ta bayar wajen tarbiyyantar da tsofaffin ɗalibanta, ba za ta iya maye gurbin duk abin da makarantar ta yi musu ba. Ya ce manufar ƙungiyar ita ce ta taimaka wajen ci gaban makarantar da samar da kyakkyawan yanayin karatu ga ɗalibai.

Ya kuma shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya mayar da hankali wajen gyara gidajen malaman makarantu, tare da tabbatar da cewa malamai suna samun masauki mai kyau, musamman waɗanda aka tura aiki daga wasu yankuna.

Ya ce ƙarancin albashi da tsadar rayuwa na ƙara wa malamai wahala wajen biyan kuɗin haya da sauran buƙatun yau da kullum, lamarin da ya kamata gwamnati ta duba domin inganta jin daɗinsu da ƙarfafa su wajen gudanar da aikinsu.

A nasa jawabin, shugaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke ɗanbatta, Alhaji Maikuɗi Garba Gwarzo, ya yaba wa gidauniyar bisa tallafin da ta bayar ga makarantar.

Ya bayyana cewa gidauniyar ta tallafa wa makarantar a shekarun 2024, 2025 da 2026, wanda ya nuna ci gaba da jajircewarta wajen tallafa wa ilimi da ɗalibai.

Alhaji Gwarzo ya ce a halin yanzu, makarantar na samun tallafi daga gwamnati da kuma ƙungiyar DOBA, yana mai bayyana muhimmancin haɗin gwiwar gwamnati da tsofaffin ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki wajen inganta ilimi.

By ukarofi

Leave a Reply