Kiran Tinubu da ‘Bola’ ba zai sauya matsayinsa na shugaba ba – Shettima

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya soki tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan yadda yake yawan kiran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sunansa na farko, yana mai cewa hakan ba zai sauya matsayinsa na Shugaban ƙasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Sojin Nijeriya ba.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa ta jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC), a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.

A yayin jawabin nasa, mataimakin shugaban ƙasar ya kuma soki yawan yunƙurin Atiku na neman shugabancin Nijeriya, tare da sukar wasu shawarwarin tattalin arziƙin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ke bayarwa.

Da yake mayar da martani kan yadda Atiku ke kiran Tinubu da sunansa na farko, Shettima ya ce matsayin Tinubu a kundin tsarin mulkin ƙasar bai sauyawa, ko da kuwa yadda abokan hamayyarsa suka zaɓi kiran shi.

“Waɗanda ke neman adalci dole ne su fara kasancewa masu gaskiya. Za ka iya kiransa Bola. Idan kana so, ka kira shi Adekunle. Amma gaskiyar magana ita ce, shi ne Shugaban ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin Tarayyar Nijeriya,” in ji Shettima.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma kwatanta yawan yunƙurin Atiku na zama shugaban ƙasa da tsohon Firaministan Kenya, Raila Odinga, wanda ya sha tsayawa takarar shugaban ƙasar amma bai yi nasara ba.

Shettima ya ce bai kamata a kwatanta Atiku da tsohon Shugaban ƙasar Amurka, Abraham Lincoln, wanda aka fi sani da rawar da ya taka wajen kawo ƙarshen bautar da mutane a Amurka ba. Lincoln ya shugabanci Amurka daga shekarar 1861 zuwa 1865, lokacin da aka kashe shi.

Duk da sukar da ya yi wa Atiku, Shettima ya ce zai ci gaba da girmama shi a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban ƙasa.

“Atiku Abubakar, zan ci gaba da girmama shi tare da kiransa tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar,” inji shi.

Ya ƙara da cewa ba zai bi sahun wasu da suke yi wa Atiku laƙabi na daban ba, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar, wanda a cewarsa ya nemi shugabancin Nijeriya har sau takwas, ba Lincoln ba ne, sai dai ya fi kama da Odinga.

Shettima ya jaddada cewa burin siyasa kaɗai bai isa mutum ya zama jagora ba, domin ana buƙatar ɗabi’a mai kyau, ladabi, kamewa da kuma fahimtar nauyin da ke tattare da riƙe muƙamin gwamnati.

Haka kuma, ya soki Peter Obi kan shawarwarinsa na tattalin arziƙi da kuma ikirarin da yake yi game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Shettima ya bayyana cewa yawan al’ummar Nijeriya, girmanta da kuma yanayin tattalin arziƙinta sun bambanta da na wasu ƙasashe, don haka ba za a iya ɗauko manufofin wasu ƙasashe a aiwatar da su a Nijeriya ba tare da la’akari da yanayin ƙasar ba.

“Ba za a iya tafiyar da ƙasa mai al’umma sama da miliyan 250 ta hanyar amfani da ƙididdiga da shawarwarin tattalin arziƙi da aka aro daga wasu wurare ba tare da la’akari da yanayin ƙasar ba,” inji Shettima.

Ya ce manufofin da suka yi aiki a ƙasar Bangladesh ba lallai ne su yi aiki a Nijeriya ba, matuƙar ba a yi la’akari da bambance-bambancen da ke tsakanin ƙasashen ba, musamman ta fuskar yawan jama’a, tsarin tattalin arziƙi da hukumomin gwamnati.

Shettima ya ce yana girmama Peter Obi, amma ya zarge shi da yin ikirarin cewa ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba tare da gabatar da hujjojin da za su tabbatar da hakan ba.

Ya kuma bayyana Obi a matsayin wanda ke amfani da ƙididdiga marasa inganci da shawarwarin tattalin arziƙi marasa daidaito, yana mai kwatanta ƙoƙarin amfani da manufofin wasu ƙasashe a Nijeriya da ƙoƙarin sanya tufafin da aka ɗinka wa ƙaramin mutum a jikin wanda ya fi shi girma.

Sai dai, duk da sukar da ya yi wa ’yan adawa, Shettima ya buƙaci mambobin Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC da su riƙa girmama abokan hamayyarsu, yana mai cewa su ’yan Nijeriya ne kuma ba abokan gaba ba ne.

“Daga yanzu har zuwa ƙarshen wannan yaƙin neman zaɓe, za mu tattauna ra’ayoyi da manufofi, amma za mu riƙa mu’amala da dukkan abokan hamayyarmu cikin girmamawa da mutunci. Ba abokan gabanmu ba ne. ’Yan’uwanmu ne, ’yan ƙasarmu ne, kuma shugabanninmu ne,” in ji shi.

Ya gargaɗi masu yaƙin neman zaɓen APC da su guji shiga musayar zagi da abokan hamayya, yana mai cewa ya kamata su mayar da martani ga suka ta hanyar gabatar da hujjoji, bayanai da dalilai masu ma’ana.

“Za mu iya mayar da martani ga ire-iren maganganun ƙarya da kuma zarge-zargen da abokan hamayyarmu ke yi, amma ba za mu faɗa tarkonsu ba. Za mu gabatar da hujjoji,” in ji Shettima.

Ya ƙara da cewa za su yi amfani da ƙididdiga da hujjoji, tare da yin muhawara bisa dalilai masu ma’ana maimakon dogaro da motsin rai, ƙarin gishiri ko ƙirƙirar ƙarya.

A ƙarshe, Shettima ya bayyana ra’ayinsa cewa Shugaba Tinubu ya cancanci samun wa’adi na biyu, yana mai cewa shirin gyare-gyaren da gwamnatinsa ta fara ya samu ci gaba wanda, a ganinsa, bai kamata a katse ba.

Ya buƙaci mambobin Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa ta APC da su kai saƙon gwamnati zuwa ga al’ummomi a faɗin Nijeriya, su saurari ra’ayoyin masu zaɓe, sannan su bayyana manufofi da ayyukan gwamnatin yayin da suke shirin zaɓen shekarar 2027.

By ukarofi

Leave a Reply